Labarai

Sojoji sun kashe babban kwamandan Boko Haram, Abu Rajab, da wasu a Sambisa

Sojoji sun kashe babban kwamandan Boko Haram, Abu Rajab, da wasu a Sambisa

Sojoji sun yi nasarar hallaka wani babban kwamandan Boko Haram Abu Rajab da wasu mutum biyu a wani sumame da suka kai dajin Sambisa. Wannan samamen ya samu haɗin gwiwar 'yan sakai inda ya faru a wani sansani na 'yan ta'addan da ke Bula Daloje, a ƙaramar hukumar Bama. Sojojin sun yi musayar wuta da ƴan ta'addan yayin da suka kashe uku daga cikinsu, yayin da saura suka tsere. A cikin waɗanda suka kashe akwai wani babban kwamandan ƙungiyar Abu Rajab wanda an jima a na neman shi. Sun yi nasarar ƙwato bindiga ƙirar Ak47 da wayoyin hannu da dama.
Read More

Yaki da cin hanci da rashawa na buƙatar taron-dangi, inji Shugaba Tinubu

Daga NASIR S. GWANGWAZO Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ƙasashen kungiyar ECOWAS su amince da kuma aiwatar da daftarin yarjejeniyar yaƙi da cin hanci da rashawa. A yayin da yake jawabi a taron shekara-shekara karo na 6 na Ƙungiyar Taron-Dangin Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Yammacin Afirka (NACIWA) a Abuja, Tinubu ya jaddada buƙatar ɗaukar ƙwararan matakai da zaƙewa a yayin yaƙi da cin hanci da rashawa da ke addabar yankin. Shugaban wanda mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta, ya sanar da bayar da gudummawar ginin ofishin dindindin ga hedikwatar kungiyar ta NACIWA, kana ya…
Read More
‘Yan bindiga sun saki bidiyon basaraken Jihar Sokoto ɗaure cikin jini

‘Yan bindiga sun saki bidiyon basaraken Jihar Sokoto ɗaure cikin jini

A wani faifan bidiyo da ya ke yawo wanda mai garin Gatawa Muhammad Bawa, yayi kira da gwamnatin Jihar da ta kawo masa agaji a hannun 'yan bindiga domin wa’adin da su ka bayar ya wuce. A faifan bidiyon, an nuna mai garin ɗaure cikin jini. mai garin ya kwana 22 kenan a hannun ƴan bindiga Duk da yanzu Jaridar Manhaja ba ta da tabbacin faifan, amma ɗan majalisar jihar mai wakiltar Sabon Birni ya tabbatar wanda ke cikin bidiyon mai garin ne. A cikin bidiyon mai garin na faɗin "ina kira ga 'yan uwana, abokai cewa yau ne wa'adin…
Read More

‘Yan sanda sun kama wata mata ɗauke da bindiga da harsasai a cikin buhun gari

Daga Umar Garba a Katsina Jami’an rundunar ƴan sanda na musamman sun kama wata mata ƴar shekara 30 mai suna Hauwa Yusuf ɗauke da bindiga ƙirar AK-47 da harsasan bindiga a cikin buhun garri. An damƙe matar ne a hanyar Abuja-Kaduna lokacin da jami'an rundunar ƴan sanda ke gudanar da buncike akan hanyar. Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar ƴan sandan STS da ke Abuja. Adejobi ya ƙara da cewa, Yusuf ta amsa cewa wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya yi ƙaurin suna a jihar Katsina, Aminu Basulluɓe…
Read More
An buƙaci Tinubu ya binciki yadda gwamnoni suka yi da bashin Dala biliyan 1.5

An buƙaci Tinubu ya binciki yadda gwamnoni suka yi da bashin Dala biliyan 1.5

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta buƙaci Shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya binciki yadda gwamnonin jihohi 36 da Birnin Tarayya Abuja suka yi amfani da bashin da suka karɓo daga Bankin Duniya. Ƙungiya ta buƙaci Tinubu ya umarci Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN) da hukumomin da ke yaƙi da cin hanci da rashawa da su gaggauta bincikar yadda aka kashe bashin na dala biliyan 1.5. Gwamnonin sun ciyo bashin ne domin rage raɗaɗin talauci da ƙara inganta jin daɗin al'umma a faɗin jihohinsu. Buƙatar bincikar gwamnonin da SERAP…
Read More
Makarantun firamaren gwamnati na cigaba da taɓarɓarewa duk da biliyoyin kuɗaɗen da aka ware

Makarantun firamaren gwamnati na cigaba da taɓarɓarewa duk da biliyoyin kuɗaɗen da aka ware

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Makarantun firamare na gwamnati a faɗin Nijeriya na ƙara taɓarɓarewa duk da cewa akwai kuɗi biliyan N54.9 na kuɗaɗen Hukumar Kula da Ilimin Bai ɗaya (UBEC) da gwamnatocin jihohi ke ci gaba da yin amfani da su. Wannan sakaci da ake ci gaba da yi ya sa iyaye a garuruwa da dama na Nijeriya ke mayar da ’ya’yansu daga makarantun gwamnati zuwa makarantu masu zaman kansu saboda taɓarɓarewar ababen more rayuwa da rashin ingancin koyarwa da makarantun gwamnati. Yayin da wasu gwamnatocin jihohin ke ikirarin ba da fifiko kan ilimin al’umma, rahotanni sun nuna cewa ya…
Read More
Shettima ya yaba wa MTN bisa gudunmawar tallafin Biliyan ɗaya

Shettima ya yaba wa MTN bisa gudunmawar tallafin Biliyan ɗaya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya yaba da gudunmawar Naira biliyan 1 ga shirin tallafin abinci na gwamnatin tarayya da na’urorin zamani guda 4,600 domin raba wa makarantu da babban kamfanin sadarwa na MTN ya bayar. Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugaban kamfanin sadarwa na MTN na Nijeriya, Ernest Ndukwe a ziyarar ban girma da ya kai fadar shugaban ƙasa. Ya ce, matakin da kamfanin na MTN ya ɗauka na ƙoƙarin da gwamnati ke yi na magance wahalhalu a ƙasar nan ya dace a yi…
Read More
Atiku ya caccaki masu yunƙurin daƙile cigaban matatar Ɗangote

Atiku ya caccaki masu yunƙurin daƙile cigaban matatar Ɗangote

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi gargaɗi kan yunƙurin da wasu mutane na ciki da na waje ke yi na kawo cikas ga cigaban matatar man Dangote. A cikin wata sanarwa da ya wallafa a akn shafinsa na ɗ a ranar Asabar, Atiku Abubakar ya bayyana matatar a matsayin wani muhimmin aiki na kamfanoni masu zaman kansu da aka sanya don biyan buƙatun gida da waje. Ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su tabbatar da cewa mutanen gida da na waje ba su hada kai don hana wasar cin moriyar matatar man ba. Sanarwar ta…
Read More
Al’ummar Kano sun yi addu’o’i kan yunwa da rashin shugabanci nagari

Al’ummar Kano sun yi addu’o’i kan yunwa da rashin shugabanci nagari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Dubban al'ummar Musulmi sun gudanar da addu'o'i na musamman na yaƙi da yunwa da wahala da kuma rashin shugabanci nagari a wurare da dama a jihar Kano. An ruwaito cewa an gudanar da zaman addu'o'i ne domin kawo ƙarshen zanga-zangar adawa da wahalhalun da ƙasar ke fama da shi na tsawon kwanaki 10 na #EndBadGovernance. A Kano, tun da farko masu gudanar da sallar sun sanar da cewa za a gudanar da taron a masallacin Isyaka Rabi’u, Goron Dutse da sauran wurare da ke faɗin ƙananan hukumomin jihar 44 a ranar Asabar ɗin da ta gabata.…
Read More
Farashin kayan abinci yana raguwa a kasuwanni – Onanuga

Farashin kayan abinci yana raguwa a kasuwanni – Onanuga

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mai Bawa Shugaban ƙasa Bola Tinubu shawara na musamman kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa hauhawar farashin kayan abinci yana raguwa. Onanuga ya bayyana cewa farashin doya da tumatur da sauran kayan abinci na raguwa matuƙa. A yayin da wallafa a shafinsa na ɗ, ya rubuta cewa, "Farashin abinci yana saukowa yayin da farashin doya, tumatir ya ragu sosai." Ya mayar da martani ne kan wani rahoto da ke cewa farashin kwandon tumatir ya ragu. Rahoton ya ce, a halin yanzu ana sayar da babban kwandon tumatur a kasuwar Ketu kan kimanin Naira 55,000…
Read More