Labarai

Badaƙala: EFCC ta sake kamo shugaban NAHCON bayan ta gano miliyoyi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati, EFCC a wani karo ta sake tsare shugaban hukumar jigilar alhazan Nijeriya (NAHCON), Jalal Arabi tare da sakatarensa, Abdullahi Kontagora, sakamakon bincike da ta ke mu su na zargin sarrafa kuɗaɗen tallafin Alhazan shekarar 2024 da adadin su ya kai Naira biliyan 90 ba bisa ƙa'ida ba. Rahotanni sun ce EFCC ta gano kuɗin Saudiya daga Arabi da wasu manyan jami'an NAHCON da adadinsu ya kai kimanin Riyal 314,098. Binciken EFCC ya nuna cewa, a na zargin Arabi ya kimtsa biyan kan sa da wasu jami'an sama da…
Read More
A yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima domin ba ƙananan hukumomi cikakken ‘yanci – Shinkafi

A yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima domin ba ƙananan hukumomi cikakken ‘yanci – Shinkafi

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Babban Daraktan ƙungiyar Patriot for the Advancement of Peace and Social Development kuma manazarcin siyasa a ƙasar nan Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya bayyana cewa akwai buƙatar gyara wasu sassan kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 da nufin baiwa ƙananan hukumomi cikakku. cin gashin kansu na kuɗi.A cewarsa, Kundin tsarin mulki na 1999 yana da tanadi “mai kyau, mara kyau, da mummuna” don haka yana buƙatar gyara. Dakta Shinkafi a wata hira da manema labarai, ya yi tsokaci kan ziyarar da wata ƙungiya mai suna Patriots ƙarƙashin jagorancin tsohon Sakatare-Janar na Commonwealth Cif Emeka Anyaoku…
Read More
Zargin ɗaukar nauyin zanga-zanga: Gwamnatin Nijeriya ta ƙwace Dala miliyan 37 daga asusun ‘yan Kirifto

Zargin ɗaukar nauyin zanga-zanga: Gwamnatin Nijeriya ta ƙwace Dala miliyan 37 daga asusun ‘yan Kirifto

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Nijeriya ta ƙwace Dala miliyan 37 daga asusun ‘yan Kirifton da ake zargi da ɗaukar nauyin zanga-zanga. A ranar 8 ga Agusta ne EFCC ta shigar da ƙorafi a kotu, inda ta bayyana cewa ‘kuɗaɗen kirifto’ kuɗaɗe ne na harƙalla, kuma ana ɗaukar nauyin ta’addanci da kuɗaɗen.” Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ce ta bayar da umarnin ƙwace kuɗaɗen daga cikin asusunsu. Mai Shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da wannan hukunci a ranar 9 ga Agusta, kuma Manhaja ta samu kwafen hukuncin. Nwete ya bada umarnin kulle asusun na su ne…
Read More
Farashin litar man fetur ya kai N950 a Kano

Farashin litar man fetur ya kai N950 a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rahotanni na cewa farashin duk lita ɗaya ta man fetur ya kai Naira 950 a Jihar Kano. Wannan na zuwa ne bayan da masu sayar da man fetur ɗin suka kara farashin duk lita ɗaya daga Naira 900 zuwa 950 a wannan Larabar. Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan dalili ya sanya masu sana’ar tuƙa Keke NAPEP a cikin birnin Dabo su ma suka ƙara farashin kuɗinsu na jigilar fasinjoji da kusan kashi 100. Lamarin dai na zuwa ne ’yan kwanaki bayan kammala zanga-zangar tsadar rayuwa ta #EndBadGoɓernanceInNigeria da aka gudanar a tsakanin 1…
Read More
Mata sun yi zanga-zanga tsirara kan rashin tsaro

Mata sun yi zanga-zanga tsirara kan rashin tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mata sun gudanar da zanga-zanga a tuɓe domin bayyana fushinsu kan matsalar rashin tsaro a yankin Akoko da ke Jihar Ondo. Matan sun gudanar da zanga-zangar ne suna masu nuna damuwa bisa yawan kashe-kashe da garkuwa da mutane da kuma lalata gonaki a yankin. Masu zanga-zangar waɗanda yawancinsu tsofaffi ne suna zargin makiyaya da hannu a kashe-kashe da kuma lalata gonaki. Sun yi tattakin nasu a tuɓe ne bayan kashe wani manomi mai suna Sunday Ayeni a yayin wani rikicin tsakaninsa da wasu makiyaya a gonarsa. A ƙarshen mako ne aka tsinci gawarsa bayan…
Read More
Tallafin Alhazai: EFCC ta tsare Shugaban NAHCON kan zargin almubazzarancin biliyan N90 

Tallafin Alhazai: EFCC ta tsare Shugaban NAHCON kan zargin almubazzarancin biliyan N90 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Hukumar Alhazai na ƙasa NAHCON, Jalal Arabi da sakataren hukumar Abdullahi Kontagora a halin yanzu suna hannun hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa bisa zargin karkatar da kuɗaɗen tallafin Hajji na N90bn na 2024. A cikin wata takarda da wakilinmu ya gani a ranar Laraba, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ce an ƙwato jimillar SR314,098 daga hannun shugaban NAHCON da sauran manyan jami’ai. Hukumar EFCC ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa daga cikin N90bn na tallafin Hajji, Arabi, ya biya…
Read More
Abbas ya janye ƙudurin hukunta waɗanda suka ƙi rera taken ƙasa

Abbas ya janye ƙudurin hukunta waɗanda suka ƙi rera taken ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas ya janye ƙudurin da ya gabatar na samar da dokar “hukunta masu ayyukan tayar da hargitsi da waɗanda suka ƙi rera taken ƙasa”. A cikin sanarwar janye ƙudurin dokar, wadda ta samu sa hannun mai taimaka wa shugaban Majalisar wakilan kan yaɗa labarai, Musa Abdullahi Krishi, ta ce an janye dokar ne “bayan tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki da kuma kyakkyawan la’akari da halin da ƙasa ke ciki.” Sanarwar ta ƙara da cewa Honorabul Abbas “ba zai taɓa goyon bayan duk wani mataki da zai yi…
Read More
Ɗiyar Gwamnan Nasarawa ta buƙaci a riƙa damawa da mata a harkokin shugabanci

Ɗiyar Gwamnan Nasarawa ta buƙaci a riƙa damawa da mata a harkokin shugabanci

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Ɗiyar Gwamnan Jihar Nasarawa, Hussaina Abdullahi Sule ta buƙaci a riƙa bai wa mata damar shugabancin jihar da ƙasa baki ɗaya suma don ba su damar bai da nasu gagaruman gudumawa ga ci gaban ƙasa baki ɗaya. Hussaina Abdullhi Sule ta yi kiran ne na musamman a wajen wani babban taron bita na mata na yini 1 wadda aka gudanar a babban ɗakin taro na babbar Jami’ar Gwamnatin Jihar (NSUK) dake birnin Keffi hedikwatar ƙaramar hukumar Keffi a jihar. Taron bitar na musamman na kwana guda mai taken: Gano mace dake cikin ki wato…
Read More
Sarkin Kabi ya nemi ‘yan siyasa da su haɗa kai don samun ci gaba

Sarkin Kabi ya nemi ‘yan siyasa da su haɗa kai don samun ci gaba

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi  Maimartaba Sarkin Kabin Argungu Allhaji Sama'ila Muhammad Mera ya yi kira ga 'yan siyasa da su haɗa kawunansu don samun ci gaba da kuma amfanin al'umma. Ya yi wannan kiran be ranar Litinin ɗin da ta gabata yayin da ayarin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen Jam'iyyar APC ya kai ziyarar ban-girma a fadar basaraken. Da ya ke jawabi, basaraken ya ce ta hanyar haɗin kai tsakanin masana da 'yan siyasa ne za a iya samun ci gaba mai ɗorewa a cikin wannan jihar. Ya ƙara da cewa yana da kyau al'umma su kuma su…
Read More

Kamfanin Chana ya yaudari kotu kan jiragen gwamnati da aka ƙwace – Nijeriya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ofishin shugaban ƙasa ya yi gamsashshen bayani game da ƙwace jirage uku masu tashin angulu na Nijeriya da wata kotun Faransa ta yi. A ranar Talata ne kotun ta bayar da umarnin ƙwace jiragen sakamakon wani yarjejeniya da aka ƙulla ba bisa ƙa'ida ba tsakanin gwamnatin jihar Ogun da kuma wani kamfanin ƙasar China. Kamfanin mai suna 'Zhongshan Fucheng Industrial Investment Co. Limited' ya shigar da ƙara kotu ne bayan da gwamnatin Ogun ta dakatar da kwantiragin yarjejeniyar gudanar da harkokin fitarwa tsakanin ta da shi a shekarar 2016.. Saidai ofishin shugaban ƙasa ya ce kamfanin…
Read More