17
Aug
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta shirya tsaf don samar da ayyukan yi miliyan uku ga matasan Nijeriya ta hanyar Shirin 3MTT. Ministan ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Litinin a Taron Matasa 'Yan Sandan Nijeriya mai taken “Inganta ƙimar Matasan Nijeriya don Tsaron ƙasa.” Ministan, wanda ya samu wakilcin Darakta Janar na hukumar gidan rediyon Muryar Nijeriya (ɓoN), Malam Jibrin Baba Ndace, ya ce shirin na 3MTT, wanda Ma’aikatar Sadarwa ke jagoranta, wani shiri ne na ilimi da ƙwarewar da za su inganta iyawa…
