Labarai

Baƙuwar cuta ta kashe mutane 13 a Zamfara

Baƙuwar cuta ta kashe mutane 13 a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Adadin mutanen da suka rasu sakamakon kamuwa da wata baƙuwar cuta ya ƙaru zuwa 13 a Jihar Zamfara. Aqalla mutane 505, akasarinsu mata da ƙananan tara ne aka kai asibiti sakamakon kamuwa da cutar a ƙananan hukumomin Gusau, Maradun da kuma Shinkafi a jihar. Haka zalika an samu ɓullar cutar a Jihar Sakkawato a ƙananan hukumomin Isa da Zurmi. A watan Fabrairu aka fara samun ɓullar baƙuwar cutar a ƙauyen Tsibiri da ke Ƙaramar Hukumar Maradun. Wani mazaunin Tsibiri ya ce daga lokacin “Zuwa ranar Lahadi 12 ga Mayu, 2024, mutane 228 ne suka…
Read More
Tinubu ya haramta sayen motoci masu amfani da fetur a ma’aikatun gwamnati

Tinubu ya haramta sayen motoci masu amfani da fetur a ma’aikatun gwamnati

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaba Tinubu ya haramta sayen motoci masu amfani da man fetur a hukumomi da ma’aikatun gwamnatin Nijeriya. Shugaban ƙasar ya kuma umarci motocin su koma amfani da ababen hawa masu amfani da iskar gas. A jawabinsa ga Majalisar Zartaswa ta Ƙasa, Shugaba Tinubu, ya ce babu gudu babu ja da baya kan batun komawa amfani da ababen hawa masu amfani da iskar gas a Nijeriya. A cewarsa, hakan na daga cikin matakan da gwamnatinsa ta ɗauka na tabbatar da wadataccen makamashi da kuma rage tsadarsa a ƙasar. Ya kuma ba da umarnin soke duk…
Read More
APC ta dakatar da Hon Aminu Sani Jaji kan yi wa jam’iyya zagon ƙasa

APC ta dakatar da Hon Aminu Sani Jaji kan yi wa jam’iyya zagon ƙasa

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC a mazaɓar Birnin Magaji dake ƙaramar hukumar Birnin Magaji, jihar Zamfara, ta dakatar da Hon. Aminu Sani Jaji daga jam'iyyar a kan yi wa jam'iyyar zagon ƙasa yayin zaɓen 2023 a jihar. Aminu Sani Jaji shi ne ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Birnin Magaji da Ƙaura Namoda na tarayya. Dakatarwa na ƙunshe ne a wata wasiƙa da aka gabatar ga shugaban jam’iyyar APC na jiha mai ɗauke da sa hannun shugaban jam’iyyar APC na mazaɓar Birnin Magaji, Alh. Bello Lawali Maizogale da Salmanu Umar Tsamiya, inda ake zargin Hon.…
Read More
Al-Nakba: Falastinawa ba za su taɓa miƙa wuya ga Isra’ila ba – Ambasada Abu Shawesh

Al-Nakba: Falastinawa ba za su taɓa miƙa wuya ga Isra’ila ba – Ambasada Abu Shawesh

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A rana ta 223 na yaƙin kisan ƙare dangi a akan al'ummar Falastinu, Jakadan Falastinu a Nijeriya Abdullah Abu Shawesh ya bayyana cewa, a cikin shekaru 76 da fara gallaza wa al'ummar Falastinu, ba mu manta ba, ba za mu yafe ba. Al'ummar Falastinawa za su ci gaba da tunkarar mamayar da Isra'ila ke yi, ba za su taba miƙa wuya ba. A wata sanarwa da ya fitar a ranar 16 ga Mayu, 2024, ya ce; "A ranar 15 ga watan Mayu al'ummar Falastinu a duk duniya sun gudanar da bukukuwan cika shekaru 76 na 'Al-Nakba'…
Read More
Majalisar Dattawa ta amince da kafa Hukumar Raya Arewa maso Yamma

Majalisar Dattawa ta amince da kafa Hukumar Raya Arewa maso Yamma

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Alhamis ne Majalisar Dattijai ta amince da ƙudirin dokar Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma domin magance ƙalubalen da jihohi bakwai ke fuskanta a yankin. Wannan ya biyo bayan la'akari da amincewa da rahoton Kwamitin Ayyuka na Musamman akan NWDC ya yi. Ƙudirin dokar wanda ya wuce karatu na uku a majalisar ya samu ɗaukar nauyin mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin, da wasu ’yan majalisa 20 daga jihohi bakwai na shiyyar Arewa maso Yamma. Shugaban kwamitin Sanata Shehu Kaka (mai wakiltar Borno ta tsakiya) wanda ya gabatar da ƙudirin, ya ce an tsara…
Read More
Nijeriya ce koma baya a kasafin ilimi a yammacin Afirka – ASUU

Nijeriya ce koma baya a kasafin ilimi a yammacin Afirka – ASUU

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, ta yi Allah-wadai da yadda ake nuna halin ko-in-kula da harkar ilimi, inda ta ce Nijeriya ce a ƙarshe a kasafin kuɗin ilimi a yankin yammacin Afirka. Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana haka a taron yini ɗaya kan ‘Bukatun Ɗalibai masu tasowa a Cibiyoyi’, wanda Asusun Tallafawa Manyan Makarantu (TETFund) ya shirya a Abuja ranar Talata. Ya kuma nanata kiran da ƙungiyar ta yi na sake duba harajin ilimi zuwa kashi 10 cikin 100, yana mai cewa za ta kara kuɗaɗen TETFund daga Naira biliyan 600 a duk shekara…
Read More
Zargin rashawa: EFCC ta sha alwashin ɗaukar mataki kan Matawalle lokacin da ya dace

Zargin rashawa: EFCC ta sha alwashin ɗaukar mataki kan Matawalle lokacin da ya dace

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Kuɗi da Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa, EFCC, ta sake jaddada aniyarta ta gudanar da cikakken bincike kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa Ƙaramin Ministan tsaro, Bello Matawalle, a lokacin da ya ke Gwamnan Jihar Zamfara. Kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata, yayin wani taro a hedikwatar EFCC da ke Abuja tare da mambobin ƙungiyar siyasa ta Tinubu Youth and Women Network, da ke fafutukar gudanar da bincike kan zargin almundahana da Matawalle. Ana tuhumar Matawalle…
Read More
ASUU na barazanar shiga yajin aiki bisa rashin kafa majalisun jami’o’i

ASUU na barazanar shiga yajin aiki bisa rashin kafa majalisun jami’o’i

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta bayyana shirin fara yajin aikin gama-gari a faɗin ƙasar domin nuna adawa da gazawar Gwamnatin Nijeriya na kafa Majalisar Gudanarwar Jami’o’in Tarayya. A yayin wani taro da aka yi a sakatariyar ASUU ta ƙasa da ke Abuja, Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana takaicinsa kan rashin kafa Majalisar Gudanarwa a dukkan jami’o’in tarayya da sauran batutuwan da ba a warware su ba. Farfesa Osodeke ya bayyaba cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta samu isasshen lokaci don magance buƙatun ƙungiyar. A watan Mayun da ya gabata ne gwamnati ta rusa majalisar…
Read More
Adadin waɗanda suka rasu a harin masallaci a Kano ya ƙaru zuwa 15

Adadin waɗanda suka rasu a harin masallaci a Kano ya ƙaru zuwa 15

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce adadin mutanen da suka mutu a harin da wani matashi ya kai wa wasu masallata a wani masallaci a Kano ya kai mutum 15, Ana zargin cewa matashin ya watsa fetur a masallacin tare da cinna wuta, sannan kuma ya kulle ƙofar masallacin, tare da mutum kusan 40 a ciki. Rahotonnin sun ce matashin ya kai harin ne sakamakon rigima kan rabon gado, Shafi’u Abubakar ya yi zargin mutanen da ya cinna wa wutar mafi yawancinsu suna cikin Masallacin kuma sun cutar da shi a rabon gadon, Tuni…
Read More
Gwamna Lawal ya yaba da ƙoƙarin sojoji wajen fatattakar ‘yan ta’adda a Zamfara

Gwamna Lawal ya yaba da ƙoƙarin sojoji wajen fatattakar ‘yan ta’adda a Zamfara

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya yaba wa dakarun haɗin gwiwa dangane da sabunta salon yaƙi da 'yan fashin daji a jihar. Sanarwa mai ɗauke da sa hannun kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ta ce, a ƙarshen makon da ya aka tura ƙarin sosjoji jihar domin ci gaba da fatattakar 'yan ta'addan da ke addabar sassan jihar. Sanarwar ta kuma bayyana ƙoƙarin da sojojin ke yi a wannan lokaci na murƙushe 'yan ta'adda a matsayin matakin da ya dace a ɗauka na ganin bayana ɓata-garin a jihar Zamfara. Sanarwar ta ce, “Aikin da sojoji ke yi a yankunan da…
Read More