Labarai

An kashe ’yan ta’adda 36, an kama 137, an ceto mutum 140 – Hedkwatar Tsaro

An kashe ’yan ta’adda 36, an kama 137, an ceto mutum 140 – Hedkwatar Tsaro

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) a ranar Alhamis ta ce, sojojin da aka tura sassa daban-daban na ƙasar sun kashe ’yan ta'adda 36, sun kuma kama ’yan bindiga 137 da kuma mara musu baya 6. Rundunar sojin ta kuma ce, sojojin sun kama mutane 15 da suka yi satar mai tare da kwato kuɗi Naura 3,177,650.00 tare da kuɓutar da mutum 140 da aka yi garkuwa da su. Daraktan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, ya kuma bayyana cewa, an ƙwato…
Read More
Mai Shari’a Rabi Umar ta nuna damuwa game da yawaitar matasa a gidajen yari a Bauchi

Mai Shari’a Rabi Umar ta nuna damuwa game da yawaitar matasa a gidajen yari a Bauchi

Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi A ƙoƙarinta na ganin ta inganta ayyukan shari'a tare da rage cunkoso a gidajen yari, babbar Mai Sharia ta Jihar Bauchi Hajiya Rabi Talatu Umar ta fara rangadin gidajen gyaran tarbiyya na Jihar Bauchi don gane wa idonta yadda alƙalai ke gudanar da ayyukansu tare kuma da duba yiwuwar rage cunkoso a gidajen yari. Ziyarar da ta fara a ranar Litinin ta ziyarci Darazo da Misau da Gamawa da Zaki da Azare da Ningi yadda a gidan gyaran tarbiyya na Gamawa ta ga matasa sama da 100 suna jiran shari'a. Don haka ta nuna rashin…
Read More
Za mu farfaɗo da yawon buɗe ido da bunƙasa al’adun mu a Kano – Tukur Sagagi

Za mu farfaɗo da yawon buɗe ido da bunƙasa al’adun mu a Kano – Tukur Sagagi

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Manajan Darakta na hukumar yawon buɗe idanu na Jihar Kano Hon. Tukur Bala Sagagi ya bayyana cewa damar da ya samu na kula da hukumar da Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ba shi ya ji daɗi, dama ce da zai taimaka wa al'umma, yarda da ƙauna ce tasa aka kira shi aka ce ya zo ya yi. Ya ce abin dai kuma abin rashin daɗi shi ne yadda suka taras da abubuwa sun lalace sun ragargaje ba ɗa'a, ba ƙima ba tsafta, ba kayan aiki a hukumar. Ya ce abin mamaki kwamfuta wannan…
Read More
Sojojin sun fatattaki ‘yan bindiga a Sakkwato da Zamfara

Sojojin sun fatattaki ‘yan bindiga a Sakkwato da Zamfara

*An kuɓutar da wasu da aka yi garkuwa da su Daga BASHIR ISAH Dakarun haɗin gwiwa na rundunar Hadarin Daji mai aikinta a jihohin Sakkwato, Katsina, Kebbi da Zamfara sun fatattaki 'yan bindiga a maɓuyarsu da ke shiyyar Arewa maso Yamma tare da kuɓutar da wasu da aka yi garkuwa da su. Kazalika, sojoji sun ƙwace wasu kayayyaki daga 'yan bindigar yayin samamen da suka haɗa da bindigogi da alburusai da babura da shanu da sauransu. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Hedikwatar tsaro ta fitar a ranar Juma'a. Sanarwar ta ce a ranar 3 ga Agusta, sojoji…
Read More
Nijeriya na shirin tura dakarunta Nijar

Nijeriya na shirin tura dakarunta Nijar

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sanar da Majalisar Tarayya a rubuce shawarar ƙungiyar ECOWAS ta bayar na ɗaukar matakin soji s'a kan Jamhuriyar Nijar. Wasiƙar Tinubu ga Majalisar ta ƙunshi har da neman izinin tura sojojin Nijeriya zuwa Nijar kamar yadda ECOWAS ta yanke. Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da ya aike wa Majalisar wadda Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanto a zauren majalisar. Sanarwar ta nuna ECOWAS ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubun ta yi tir da matakin juyin mulkin da sojoji suka ɗauka a ƙasar ta Nijar. Ta ƙara da cewa, biyo bayan taron da ECOWAS ta…
Read More
Nijar ta yanke alaƙa da maƙwabciyarta Nijeriya

Nijar ta yanke alaƙa da maƙwabciyarta Nijeriya

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ƙarƙashin jagorancin sojijin juyin mulki, ta sanar da yanke alaƙa da Nijeriya bayan da ƙoƙarin ECOWAS na samar da maslaha a ƙasar ya ci tura. ECOWAS ta bai wa sojojin da suka yi juyin mulkin wa'adin mako guda a kan su maida Mohamed Bazoum kan kujerarsa ko kuma a yaƙe su da ƙarfin soji. A ranar Alhamis da ta gabata Shugaba Bola Tinubu a matsayinsa na Shugaban ƙungiyar ECOWAS, ya tura tawaga ta musamman ƙasar Nijar domin tattauna maslaha. Tawagar ta tafi Nijar ɗin ne ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Nijeriya, Janar Abdulsalami Abubakar (rtd) inda ta gana…
Read More
Tinubu ya cire sunan Maryam Shetty daga ministocinsa

Tinubu ya cire sunan Maryam Shetty daga ministocinsa

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya cire sunan Maryam Shetty daga jerin waɗanda yake so ya naɗa muƙaman ministocinsa sannan ya zaɓo wasu guda biyu, wato Festus Keyamo da Dr Mariya Mairiga Hakan ya bayyana ne a lokacin da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya karanto wasiƙar da Shugaban Kasa yayin zaman majalisar a ranar Juma'a. Ƙarin bayani na tafe....
Read More
Mashaya za su ɗanɗana kuɗarsu a Nijeriya sakamakon tashin farashin sinadarin giya

Mashaya za su ɗanɗana kuɗarsu a Nijeriya sakamakon tashin farashin sinadarin giya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Masu shan barasa a Nijeriya za su fuskanci matsanancin ƙarin kuɗi, kamar yadda Kamfanin Breweries na Nijeriya (NB PLC) ya sanar da ƙarin farashin kayayyakin sa daga ranar 10 ga Agusta, 2023. Kamfanin NB PLC ya yanke hukuncin ne a wata wasiƙa mai kwanan wata 1 ga Agusta 2023. Kamfanin ya ba da misali da buƙatar sake duba farashin saboda cigaba da hauhawar farashin kayayyaki da kuma wajibcin rage tasirinsa. "Muna sanar da ku cewa za mu sake nazarin farashin barasa daga ranar Alhamis 10 ga Agusta 2023." Yayin da hauhawar farashin kaya ya kai kashi…
Read More
El-Marzuq ya yi murabus daga muƙaminsa a APC saboda hawan Ganduje shugabancinta

El-Marzuq ya yi murabus daga muƙaminsa a APC saboda hawan Ganduje shugabancinta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mai Bai Wa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Shawara Kan Harkokin Shari’a, Ahmed El-Marzuk, ya yi murabus daga kwamitin zartarwa na jam’iyyar na ƙasa. Majiyar Blueprint Manhaja ta ta samu labarin cewa ya yi murabus ne a ranar Larabar da ta gabata, sakamakon dagewar da wasu abokan aikinsa suka yi na cewa ba zai iya ci gaba da zama a ofis ɗin ba saboda wasu zarge-zargen da ake masa. Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Bisa abubuwan da ke faruwa a cikin babbar jam’iyyarmu ta APC, inda mai girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje…
Read More
Ko Mbappe zai iya komawa Chelsea?

Ko Mbappe zai iya komawa Chelsea?

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rahotanni sun ce ƙungiyar Paris St-Germain ta bai wa Kylian Mbappe wa'adin sabunta kwantiragi a ranar 1 ga watan Agusta ko kuma ya bar ƙungiyar. Ana raɗe-raɗin cewa ɗan wasan na Faransa, mai shekara 24, ya amince ya koma Real Madrid a kakar wasa mai zuwa a kyauta idan kwantiraginsa a PSG ya ƙare. Mbappe na damar barin PSG a kakar bana - ko dai a matsayin aro ko kuma a kan kwangilar dindindin, wanda ta hakan ne PSG za ta iya samun kuɗi a kansa. Sai kuma yanzu ga Chelsea da Barcelona na nuna sha'awar…
Read More