Labarai

Zanga-zangar gamagari: Babu gudu ba ja da baya, cewar NLC

Zanga-zangar gamagari: Babu gudu ba ja da baya, cewar NLC

Daga BASHIR ISAH Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta ce babu gudu ba ja da baya dangane da zanga-zangar da ta ƙudiri aniyar gudanarwa kan cire tallafin mai. Shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero ne ya shaida wa manema labarai hakan jim kaɗan bayan kammala taro da Kwamitin Shugaban Ƙasa kan rage raɗaɗin cire tallai mai da aka gudanar ranar Litinin a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Ya ce shirinsu na ma'aikata su shiga zanga-zangar lumana ya zuwa ranar Laraba na nan bai canza ba. Ajaero ya ƙara da cewa, yana da yaƙinin ɓatagari ba za su yi…
Read More
Ina duba yiwuwar ƙarin albashin ma’aikata – Tinubu

Ina duba yiwuwar ƙarin albashin ma’aikata – Tinubu

Daga WAKILINMU Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Nijeriya ya bayyana cewa nazarin yiwuwar yi wa ma'aikata ƙarin albashi. Ya bayana haka ne a jawabin da ya yi wa 'yan ƙasa da yammacin ranar Litinin. Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta ɗauki tsauraran matakai ne saboda sun zama dole, “kuma babu waɗanda suka fi su sauƙi.” Ya ce, “Da a ce akwai hanyoyin da suka fi su sauƙi da na bi. “Abin da zan iya yi kawai shi ne ɗaukar matakan da za su sauƙaƙa yanayin. “Gwamnatina za ta tabbatar da yin aiki tare da dukkan jihohi don rage raɗaɗin da…
Read More
Gidauniya ta bai wa Hajiyar da ta maido da tsintuwar N84m tallafin N250,000

Gidauniya ta bai wa Hajiyar da ta maido da tsintuwar N84m tallafin N250,000

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Gidauniyar TY Buratai Humanitarian Foundation da ke da shelkwata a Jihar Nasarawa, ta bayar da gudunmawar Naira 250,000 ga Mahajjaciyar jihar Zamfara, Hajiya Aisha Muhammad Yanguru Nuhuche, wadda ta tsinci Dala 80,000 kwatankwacin sama da Naira miliyan 84 sannan ta maida kuɗin ga mahukunta a ƙasa mai tsarki. Gidauniyar ta kuma karrama ta da takardar shaidar karramawa a matsayin Jakadiyar Gaskiya. A nasa jawabin shugaban gidauniyar, Hon. Ibrahim Dahiru Ɗanfulani a hedikwatar hukumar alhazai ta jihar Zamfara da ke Gusau, ya bayyana cewa, abin da Hajiya A’isha ta yi ta cancanci yabo. Ya ce, an…
Read More
Kano: Za a kammala titin Wuju-wuju, Kasuwar Kwankwaso nan ba da daɗewa ba – Kwamishina

Kano: Za a kammala titin Wuju-wuju, Kasuwar Kwankwaso nan ba da daɗewa ba – Kwamishina

Daga RABIU SANUSI a Kano Kwamishinan Ma'aikatar Bibiyar Ayyuka da Nazari na Jihar Kano, Hon Ibrahim Namadi Dala, ya tabbatar da yunƙurin gwamnati Jihar Kano wajen ƙarasa ayyukan da ta sa gaba na Titin Wuju-Wuju da Kasuwar Zamani dake Garin Kwankwaso a Ƙaramar Hukumar Madobi da ma wasu ayyukan. Ibrahim Namadi ya bayyana haka ne ga manema labarai a ranar Laraba yayin da ya fita rangadin duba ayyukan da ba a kammala ba da aka fara tun lokacin Dr Rabiu Musa Kwankwaso da tsohuwar gwamnatin Ganduje ta yi watsi da su. Namadi ya ce, babu abun bacin rai da ya…
Read More
Tinubu zai yi wa ‘yan ƙasa jawabi a yau

Tinubu zai yi wa ‘yan ƙasa jawabi a yau

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai yi wa 'yan ƙasa jawabi da misalin ƙarfi 07:00 na dare yau Litinin. Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da ta fito ta bakin mai bai wa Tinubu shawara kan ayyuka na musamman da harkokin sadarwa, Dele Alake. Sanarwar ta ce ana buƙatar gidajen talabijin da rediyo da sauransu, da su jona da Tashar Talabijin ta Ƙasa da kuma Tashar Rediyo ta ƙasa don yaɗa jawabin Shugaba Ƙasar kai tsaye. Sai dai sanarwar ba ta fayyace dalilin da ya sa Tinubun zai yi 'yan ƙasa jawabin ba.
Read More
Yajin aiki: Ba mu yarda da ƙarin albashin 25% ba – Likitoci

Yajin aiki: Ba mu yarda da ƙarin albashin 25% ba – Likitoci

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NARD) ta ƙi amincewa da ƙarin kashi 25 na albashi da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi don inganta albashin likitoci. Ƙungiyar ta ɗauki matakin ƙin amincewar ne a wajen taron shugabanninta na ƙasa (NEC) da ya gudana a Legas, inda ta fitar da bayanin sakamakon taro a ranar Asabar mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar na ƙasa, Orji Emeka Innocent da sakatarenta na ƙasa, Chikezie Kelechi da kuma Umar Musa. Likitocin sun dage kan cimma ainihin buƙatunsu da suka haɗa da cikakken aiwatar da tsarin albashi na CMSS da aka amince…
Read More
Tsohuwar matar sarki ta maka Sarkin Dutse, Hamim Sanusi a kotu kan batun gado

Tsohuwar matar sarki ta maka Sarkin Dutse, Hamim Sanusi a kotu kan batun gado

Daga WAKILINMU Tsohuwar matar Sarkin Dutse, Hajiya Asiya Nuhu Sanusi, ta maka Sarkin Dutse, Ahaji Hamim Nuhu Sanusi, a Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a kan abin da ya shafi gado. Asiya tare da wasu mutum bakwai sun maka Sarki Hamim Nuhu Sanusi da wasu mutum shida a kotu ne inda suke ƙalubalantar hukuncin da Kotun Upper Shari’a 1, ƙarƙashin jagorancin Khadi Ado Birnin Kudu ta yanke kan batun gadonsu. Jaridar News Point Nigeria ta rawaito cewar, ƙarar wadda suka shigar ta hannun Barista Abdulhali Ali Esq, ta haɗa da Kotun Upper Shari’a 1 inda a nan aka fara shigar da…
Read More
Tinubu ya naɗa Malagi, El-Rufai, Wike muƙamin minista

Tinubu ya naɗa Malagi, El-Rufai, Wike muƙamin minista

*An kasa samun matsaya kan ministocin Kano, Zamfara da Kebbi Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ƙarshe dai Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunayen mutane 28 da ya zaɓa a matsayin ministoci, domin naɗa su a matsayin mabobin Majalizar Zartarwar Tarayyar Nijeriya. Bayan an daɗe ana jiran jerin sunayen ne a jiya Alhamis Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya zo zauren majalisar da ƙarfe 12:05 na rana, inda bayan an yi addu’ar buɗe zaman zauren sai kuma ya bayyana cewa, majalisar za ta shiga wani zama na musamman. Bayan zaman ne ya fito ya bayyana jerin sunayen…
Read More
Shugabancin APC: NPCF ta yi na’am da naɗin Ganduje

Shugabancin APC: NPCF ta yi na’am da naɗin Ganduje

Daga BASHIR ISAH Kwamitin gudanarwa na ƙasa na ƙungiyar kansilolin jam'iyyar APC (NPCF) ya amince da naɗin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin sabon Shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa. Ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Hon Muslihu Yusuf Ali, ta bayyana haka ne cikin sanarwar manema labarai da ta fitar mai ɗauke da sa hannnun Sakataren Ƙungiyar na Ƙasa, Hon Abayomi A. Kazeem da kwanan wata 29 ga Yuli, 2023. A cewar ƙungiyar, bai wa Ganduje shugabancin jam'iyyar ya yi daidai kasancewar gogaggen ɗan siyasa, ƙwararre wanda ya samar da ɗimbin cigaba a Jihar Kano a zamanin gwamnatinsa. Daga…
Read More
Ɗan El-Rufai ya samu shugabancin kwamitin Majalisa Wakilai

Ɗan El-Rufai ya samu shugabancin kwamitin Majalisa Wakilai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Alhamis ne aka naɗa Muhammad Bello El-Rufai, ɗan tsohon gwamnan Jihar Kaduna da kuma ɗiyar tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori, Erhiatake Ibori-Suenu, a matsayin shugabannin kwamitoci na dindindin. Kakakin Majalisar Abbas Tajuddeen ne ya sanar da kwamitoci 134 na dindindin a zaman majalisar. Yayin da aka naɗa ɗiyar Ibori a matsayin shugabar kwamitin majalisar wakilai na hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC), an bayyana ɗan El-Rufai a matsayin shugaban majalisar dokokin banki. Tsohon mataimakin kakakin majalisar, Ahmed Idris Wase, tsohon shugaban majalisar, Alhassan Ado Doguwa, Yusuf Adamu Gagdi, Mukhtar Betara suma sun zama…
Read More