29
Jul
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama tsohon ministan sufurin jiragen sama a gwamnatin Muhammadu Buhari, Hadi Sirika wanda ya yi amfani da jirgin saman Ethiopia wajen zamba a Nijeriya kimanin Naira biliyan 139.3. Rahotanni sun bayyana cewa, Sirika ya isa hedikwatar DSS da ke Abuja domin amsa tambayoyi a wata mota ƙirar Range Rover SUV a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, 2023. Rahotanni sun ce jami’an DSS sun yi tsare sa na tsawon sa’o’i. Wannan tuhumar na zuwa ne bayan da muƙaddashin Manajan Daraktan Kamfanin na Nijeriya Air, Captain Dapo Olumide,…
