Labarai

Makon gobe Majlisa za ta fara tantance sunayen ministocin Tinubu

Makon gobe Majlisa za ta fara tantance sunayen ministocin Tinubu

Daga BASHIR ISAH Majalisar Dattawa ta ce ya zuwa ranar Litinin mai zuwa za ta fara tantance sunayen mutum 28 da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya aike mata wanda yake neman naɗa su muƙaman ministoci. Mai magana da yawun Majalisar, Sanata Adeyemi Adaramodu (APC-Ekiti), shi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis a Majalisar ta Dattawa. Adaramodu ya ce duk da dai Litinin ba ranar zaman majalisar ba ce, amma la'akari da muhimmancin da ke tattare da aikin "ya sa muka dakatar da dokokinmu domin fara aikin tantancewar Litini mai zuwa." Ya ƙara…
Read More
Zan ƙarasa ayyukan Kwankwaso da Ganduje ya ƙi yi – Gwamna Abba

Zan ƙarasa ayyukan Kwankwaso da Ganduje ya ƙi yi – Gwamna Abba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta na ci gaba da ayyukan da tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fara a lokacin yana gwamnan jihar amma gwamnatin da ta shuɗe ta Abdullahi Ganduje ta yi watsi da shi. Kwamishinan ayyuka da gidaje na jihar Kano Marwan Ahmad ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a ofishinsa ranar Alhamis. Ya bayyana buqatar sake dawo da ayyukan a matsayin hanyar da ta dace don samar da guraben ayyukan yi ga matasa a jihar domin kame masu tada zaune tsaye a cikin…
Read More
Ministoci: Sunan mawallafin jaridun Blueprint, Manhaja ya leƙo a sunayen da Tinubu ya miƙa wa Majalisa

Ministoci: Sunan mawallafin jaridun Blueprint, Manhaja ya leƙo a sunayen da Tinubu ya miƙa wa Majalisa

Daga BASHIR ISAH Sunan mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya leƙo a rukunin farko na sunayen da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dattawan don tabbatar da su a muƙaman ministoci. Tinubu ya miƙa sunayen ga majalisa ne ta hannun Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa, Hon Femi Gbajabiamila, a ranar Alhamis. Sunayen mutum 28 Tinubu ya miƙa wa majalisar da suka haɗa da: Abubakar Momoh, Ambasada Yusuf Maitama, Tukur, Arch. Ahmed Dangiwa, Barr. Hannatu Musawa da Chief Uche Nnaji. Sai kuma Dr. Berta Edu, Dr. Dorris Aniche Uzoka, Nyesom Wike, Badaru Abubakar, Nasiru Ahmed…
Read More
Kotu ta yi watsi da buƙatar DSS ta neman ci gaba da tsare Godwin Emefiele

Kotu ta yi watsi da buƙatar DSS ta neman ci gaba da tsare Godwin Emefiele

Daga BASHIR ISAH Wata Babbar Kotu mai zamanta a birnin tarayya, Abuja, ta yi watsi da ƙarar da hukumar tsaro ta DSS ta shigar inda take buƙatar kotu ta tsawaita mata damar ci gaba da tsare tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, (CBN), Godwin Emefiele. A ranar Laraba 25 ga Yuli, DSS ta shigar da ƙarar tata a kotun, inda ta yi iƙirarin cewa ta samo ƙarin hujjar da za ta yi amfani da ita a kan Emefiele a gaban kotu. Sai dai, Kotun ta yi watsi da ƙarar ta DSS saboda rashin hurumin sauraron ƙarar. Alƙalin kotun, Hamza Muazu, ya…
Read More
Tinubu ya gabatar wa Majalisar Dattawa sunayen ministocinsa

Tinubu ya gabatar wa Majalisar Dattawa sunayen ministocinsa

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa Majalisar Dattawa sunayen waɗanda yake so ya naɗa ministoci don neman amincewarta. Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, shi ne ya gabatar da sunayen ga majalisar a ranar Alhamis. Daga jerin sunayen da aka habatar wa majalisar har da na wasu tsoffin gwamnoni da sauransu. Ga jerin sunayen kamar haka: Abubakar MomohYususf Maitama TukurAhmad DangiwaHannatu MusawaUche NnajiBetta EduDr. Diris Anite UzokaDavid UmahiEzenwo Nyesom WikeMuhammed Badaru AbubakarNasir El RufaiEkerikpe Ekp[oNkiru OnyejiochaOlubunmi –Stella OkoteteUju KEnedy OhaneyeBello Muhammad GoronyoDele AlakeLateef FagbemiMohammad IdrisOlawale EdunWaheed AdebanwpImaan Suleman IbrahimProf Ali PateProf Joseph UsevAbubakar KyariJohn…
Read More
Tinubu ya yi gargaɗi kan yunƙurin juyin mulki a Nijar

Tinubu ya yi gargaɗi kan yunƙurin juyin mulki a Nijar

Daga BASHIR ISAH Shugaban Nijeriya kuma Shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), Bola Ahmed Tinubu, ya yi gargaɗin cewa ECOWAS ba za ta yarda da duk wani al'amari da zai haifar da cikas ga zaɓaɓɓiyar gwamnati a yammacin Afirka ba. Tinubu ya yi wannan gargaɗi ne a matsayin martani kan fargabar yiwuwar juyin mulki a Jamhuriyar Nijar inda sojojin ƙasar suka tsare Shugaban Ƙasar, Mohamed Bazoum. Ya yi gargaɗin ne a matsayinsa na shugaban ECOWAS, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, inda ya bayyana datse fadar shugaban ƙasar Nijar da sojojin suka yi a matsayin…
Read More
Likitoci sun tsunduma yajin aiki

Likitoci sun tsunduma yajin aiki

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Likitocin Nijeriya (NARD) ta fara yajin aiki a wannan Laraba. Shugaban ƙungiyar, Dr Emeka Orji, shi ne ya bayyana haka ga majiyarmu ranar Talata, inda ya ce likitoci za su tsunduma yajin aiki ranar Laraba, 26 ga Yuli, 2023 da misalin ƙarfe 12 na tsakar dare. Orji ya ce, sun cim ma matsayar shiga yajin aikin ne a wajen taron shugabannin ƙungiyar da ya gudana cikin Yuli a Legas. Ƙungiyar ta ce mabobinta sun shiga yajin aikin ne domin cim ma buƙatunsu a wajen gwamnati. Ta ce buƙatun mambobin nata sun haɗa da neman a biya…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe farar hula 26, sojoji 7 a Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe farar hula 26, sojoji 7 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Aƙalla mutane 26 ne wasu ‘yan bindiga suka kashe tare da wasu sojoji bakwai a ƙauyen Kangon Garacci da ke ƙarƙashin gundumar Ɗangulbi a ƙaramar hukumar Maru a Jihar Zamfara. Wani Mazaunin yankin mai suna Malam Bello Ɗangulbi, shi ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da Blueprint Manhaja ta yi da shi ta waya a ranar Talata. A cewarsa, ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar ne da misalin karfe 04:00 na yammacin ranar Litinin. Ya ce, ‘yan bindigar da ke ƙarƙashin ƙasurgumin ɗan ta'addan nan da ya addabi yankin da aka fi sani da Ali…
Read More
DSS ta sake tsare Emefiele jim kaɗan bayan Kotu ta ba da belinsa

DSS ta sake tsare Emefiele jim kaɗan bayan Kotu ta ba da belinsa

Daga BASHIR ISAH Jami'an DSS sun dake tsare dakataccen Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, bayan rikita-rikuta da jami'an kula da gidan gyaran hali. Manjaha ta tattaro cewar an sake tsare Emefiele ne jim kadan bayan da Babbar Kotun Tarayya a Legas ƙarƙashin jagorancin Alƙali Nicholas Oweibo ta ba da belinsa kan Naira miliyan 20. Yayin zaman Kotun a ranar Talata Alƙali Oweibo ya ba da umarnin a tsare Emefiele a kurkuku har sai ya cika sharuɗɗan belin da aka gindaya masa. Jim kaɗan bayan hukuncin ne sai jami'an DSS suka shirya kansu a wajen kotun inda suka sake…
Read More