25
Jul
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar Hisba ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Sheikh Aminu Daurawa, ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da yunƙurin shirya auren jinsi a jihar. Rahotanni sun nuna cewa Kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar. Ya bayyana a wani faifan bidiyo cewa an ga wasu samari biyu masu suna Khalifa da Abubakar suna ƙoƙarin sumbatar juna a yayin wani biki, wanda ake zargin bikin aurensu ne. Sai dai waɗanda ake zargin sun musanta zargin, inda suka ce taron…
