Daga BASHIR ISAH
Kotun sauraren ƙararrakin zaɓe mai zamanta a Kano, ta tabbatar da sanar da Sanata Rufa’i Hanga ya samu a zaɓen da ya gabata a matsayin mai wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa.
Majiyarmu ta ruwaito cewa ɗan takarar Jam’iyyar APC na sanatan Kano ta Tsakiya a zaɓen da aka gudanar 25 ga Fabrairun da ya gabata, Abdulsalam Abdulkarim Zaura, shi ne ya shigar da ƙara kotu inda ya ƙalubalanci ayyana ɗan takarar jam’iyyar NNPP, Rufa’i Hanga, da hukumar zaɓe INEC ta yi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Zaura, ta hannun lauyansa, Ishaka Dikko (SAN), ya buƙaci kotun da ta yi watsi da bayyanawar da INEC ta yi sannan ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Ya yi zargin cewa zaɓen Kano ta Tsakiya cike yake da maguɗi da kuma take Dokar Zaɓe.
Sai dai a nasu martani, masu kare kansu, wato INEC da NNPP da Hanga da kuma Ibrahim Shekarau sun ce zaɓen ya gudana daidai da tanadin doka.
Da take yanke hukunci a ranar Litinin, kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a I.P Chima, ta ce, “Tun da mai ƙara ya gaza ba da hujjoji game da rashin bin Dokar Zaɓe ta 2022 da ya ce an yi, don haka an kori ƙarar.
“Haka nan, mai ƙarar zai biya mai kare kansa na farko, NNPP, Naira 300,000, sannan ya sake biyan Naira 300,000 ga masu kare kansu na biyu, na uku da na huɗu.”