Dandalin shawara: Mijina ba ya son haihuwa

(Ƙarshen wannan tambaya)

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Salam. Ina wuni Asas. Allah Ya taimake ki ga dukan lamuranki. Ki taimake ni, yadda Allah ya taimake ki. Mijina da muka yi aure da shi shekara takwas.

Da aka kawo ni gidanshi, kullum sai ya ba ni magani zai kusance ni, bai tava fashi ba, sai da na yi shakara biyu da aure, har shan maganin ya ishe ni, amma ko na yi ƙorafi sai ya rarashe ni, idan na qiya sai ya ƙi kusanta ta ko da kuwa ya matsu da son yi.

To da iyaye suka fara zancen ba mu haihu ba, mu tafi asibiti, shi ne fa ya sanar da ni ba ya son haihuwa, kuma maganin da yake ba ni na kar na ɗauki ciki ne.

Da daɗin baki ya yaudare ni na biye ma shi har muka ƙara shekara biyu. Da hankali ya saukar min sosai na fara tunanin abinda zai faru gaba idan na ci gaba da rayuwa a haka.

Ana nan sai likitan da muke zuwa ya bada shawarar na yi tsarin iyali da ake yi a asibiti, don maganin bai kamata na ci gaba da shan shi ba. Ko na sa roba, ko a ɗaure bakin mahaifa da dai wasu da ya yi bayani.

Shi ne fa da na dawo na shedama wata abokiyata, ta gaya min akwai yiwar na samu matsala idan na yi a gaba. Ba ma shi ya fi tada min da hankali ba kamar da ta ce akwai yiwar na samu kansa idan na yi, to kuma muna da kansa a gidanmu kinga Ina samun ta cikin sauƙi.

To da na gaya mishi mu nemi wata mafita ba wannan ba, shi ne fa ya ce babu wata hanya idan ba wannan ba, kuma dole zan zaɓa, ko yin ko kuma a bakin aurena. Kuma ya gaya min Allah zai fushi da ni idan har na yi sanadiyyar mutuwar aurena da kaina, kuma zai iya ma zama silar shiga ta wuta, don Annabi Muhammad sallallahu allaihi wa salam ya ce, macen da ta nemi saki daga mijinta ko qanshin aljanna ba za ta ji ba.

Wallahi ban san abin yi ba, shi ne na ce bari na neme ki, don na ga shawarar da ki ka ba wa wata a facebook sati uku da suka wuce. Allah Ya biya ki da aljanna.

AMSA:

Abu na biyu, zancen rashin son haihuwar ita kanta a matsayinki ta mace, wata babbar kuskure ne da tun anan duniya ake iya girba, duba da cewa, haihuwa na cikin da’ira ta rayuwa, yau za ki haihu, kina lalaɓa jinjirin sakamakon rashin ƙwarin jikinsa, amma idan kin yi yawancin rai za a kai wannan jinjirin ne zai zama uwa a gare ki. A yayin da ƙarfinki ya ƙare, za ki koma tamkar ƙaramin yaro, ‘ya’yanki ne masu kwatanta makamancin abinda ki ka yi masu a ƙurciyarsu.

Su ciyar da ke, bayan sun nemo, su kula da ke yayin da ki ka kwanta ciwo, su yi haƙuri da faɗa da ruɓewar tsufa da za ki masu. Idan ba ‘ya’yanki ba wa ki ke sa ran zai ma ki hakan. Kinga kuwa kina buƙatar sauya tunani kan hanyar da ki ka ɗauka.

Idan mun je gaba, zancen tsinuwa ko rashin shiga aljanna da ya yi ma ki barazana da shi ƙarya ne. Tabbas akwai hadisi na manzon rahma da ya ce, ba zata ji ko qamshin aljanna ba, macen da ta nemi mijinta saki, sai dai da sharaɗi, kamar yadda hadisin ya faɗa “macen da ta nemi saki ba tare da dalili ba.”

Addinin Musulunci ba azallumin addini ne ba, kuma ba addinin da ya yi wa mace adalci kamar sa, yadda miji ke da haqqi kanki, haka ke ma ki ke da, ciki kuwa har da neman rabuwa idan rayuwar ta sava wa addininki ko ta tava lafiya ko zuciyarki.

Hadisi ingantacce ya tabbata daga fiyayyen halitta, Annabin Larabawa da baqar fata, manzon rahma (S.A.W) cewa, “babu ɗa’a ga abin halitta wurin saɓa wa mahalicci.”

Abin nufi anan duk wani daga mutane, duk daraja da ƙimar da addini ya ba shi, kamar miji, uwa ko kuma uba, ba a amince ki yi masu biyayya ba idan sun umurce ki da yin abinda Allah Ya hane ki da yin sa.

Anan kuwa za mu iya cewa wannan matsala ta ki ta shigo ciki, idan kin qi amincewa da qudurin mijinki, da masaniyar zai sake ki idan kin yi hakan, ‘yar’uwa kwashe kayanki ki nufi gidan tsohonki hankali kwance, domin ba abinda ya taɓa alaƙarki da shiga aljanna, sai dai fa idan akwai wata taɓarar da ki ke aikatawa da zata shiga tsakaninki da shiga aljanna, wannan kam ba ta a layin.

Ƙaddarta ma ke ce ki ka nemi sakin kan dalilin ba ya son haihuwa ke kuma kina so, ko ya tursasa ki yin tsarin iyali ke kuma ba ki so, sai ki ka nemi ya sake ki, shi ma wannan ba shi da komai kuma bai taɓa komai daga addininki ba.

Daga ƙarshe zan ba ki shawarar ki samu lokacin ubangijinki, ki bazama neman ilimin addininki, ki san yadda ya kamata ki gudanar da rayuwarki, wanda hakan zai hana wani amfani da addinin wurin saka ki abinda ba ki yi niyya ba.

Sa’annan Ina fatan ki zaɓi kanki fiye da mijinki, ki zaɓi zama silar cigaban al’umma ta hanyar ƙyanƙyashe naki ɗiyan don samun ƙari a al’ummar duniya. Kada ki bari wani ya haramta miki abinda Allah Ya halasta ma ki.

Ki tsayu kan son samun naki jinin, ki yi ƙoƙarin shawo kan mijinki idan abinda yiwuwa ne, ta hanyar kwaɗaita masa haihuwar ku samu ko kaɗan ne, idan hakan bata yiwu ba, ki zaɓi bin Allah, shi zai ba ki makwafin sa, domin tun a farko shi ya ba ki shi, ba iyawarki ba.

Don haka zai iya ba ki wanda ya fi shi, domin a wurin Allah komai mai yiwa ne.