Tinubu ya yi gargaɗi kan yunƙurin juyin mulki a Nijar

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Nijeriya kuma Shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), Bola Ahmed Tinubu, ya yi gargaɗin cewa ECOWAS ba za ta yarda da duk wani al’amari da zai haifar da cikas ga zaɓaɓɓiyar gwamnati a yammacin Afirka ba.

Tinubu ya yi wannan gargaɗi ne a matsayin martani kan fargabar yiwuwar juyin mulki a Jamhuriyar Nijar inda sojojin ƙasar suka tsare Shugaban Ƙasar, Mohamed Bazoum.

Ya yi gargaɗin ne a matsayinsa na shugaban ECOWAS, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, inda ya bayyana datse fadar shugaban ƙasar Nijar da sojojin suka yi a matsayin al’amari mara daɗi.

Sanarwar ta ce, “Muna lura da yadda lamurra ke faruwa a Nijar, kuma za mu yi dukkan mai yiwuwa wajen tabbatar da komai na gudana kan tsarin dimukraɗiyya a yankin.

“Ina tuntuɓar sauran shugabannin da ke yankin kuma za mu kare dimokraɗiyyarmu daidai da tanadin doka.

“A matsayina na Shugaban ECOWAS kuma Shugaban Ƙasa, ina mai faɗa da babbar murya cewa, Nijeriya na tare da zaɓaɓɓiyar gwamnatin Nijar, kuma shugabannin yankin za mu yi tsayin daka wajen kare matsayarmu da dokarmu,” in ji Tinubu.

A ranar Labara da safe wasu sojojin da ke gadin Fadar Shugaban Ƙasar suka datse shiga fadar sannan suka tsare Shugaban Ƙasa Bazoum.