26
May
Daga UMAR GARBA a Katsina Hukumar Alhazai ta Jihar Katsina, ta bayyana cewar ta kammala shirye-shiryen fara jigilar maniyyata na shekarar 2023 daga jihar zuwa ƙasa mai tsarki. Babban Daraktan hukumar, Alhaji Suleiman Nuhu Kuki ne ya sanar da hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya a ɗakin taronta, da ke kan hanyar zuwa filin jirgin sama na Malam Umaru Musa 'Yar'adua da ke Katsina. Ya ce a ranar 29 ga watan Mayu, 2023 hukumar za ta fara jigilar maniyyatan jihar. Kuki ya kuma yaba wa masu ruwa da tsaki waɗanda suka nuna sadaukarwa don…
