27
May
Gwamnantin Tarayya ta ayyana Litinin, 29 ga Mayu a matsayin ranar hutun gama-gari ga ɗaukacin ma'aikata a faɗin ƙasa. Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, shi ne ya bayyana haka a madadin gwamnatin ranar Juma'a a Abuja. Babban Sakataren Ma'aikatar, Dokta Shuiab Belgore, ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin bai wa 'yan Nijeriya damar shagalin bikin rantsar da zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Nijeriya na 16. Sakataren ya ce, “Ministan na taya 'yan Nijeriya murnar wannan al'amari mai muhimmnci, tare da yaba musu game da tsayin dakan da suka yi wajen zaɓen da ya bai wa Bola Tinubu da mataimakinsa…
