ASUU ta tsunduma yajin aiki a Binuwai

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) reshen Jami’ar Jihar Binuwai ta sanar da fara yajin aikin sai baba-ta-gani.

Shugaban ASUU na Jami’ar Jihar (BSU), Dokta Kwaehfan Tarmombo, shi ne ya sanar da hakan ranar Juama’a.

Tarmombo ya alaƙanta yajin aikin nasu da matsalolin da mambobin ƙungiyar ke fuskanta da shugabancin jami’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *