Newcastle za ta shiga gasar Zakarun Turai karon farko cikin shekaru 20

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Newcastle ta samu damar kaiwa matakin iya taka leda a gasar kofin Zakarun Turai karon farko cikin shekaru 20, kasa da kakar wasa biyu bayan ƙungiyar ta kwaci kanta da kyar daga rukunin ’yan daga aji na teburin firimiya, wanda ya kai ga sayar da ita.

Newcastle United dai na shirin kammala kakar ta bana a matsayin ta 3 a teburin firimiyar Ingila bayan da ta yi canjaras da Leicester City a jiya Litinin wanda ke nuna yanzu ta na da maki 70 ne bayan doka wasanni 37 tazarar maki 1 tsakaninta da Manchester United wadda ta doka wasanni 36.

Rabon da Newcastle United ta doka wasannin gasar ta kofin Zakarun Turai tun shekarar 2003, batun da Eddie Howe ke bayyana cewa sam a farkon kaka ƙungiyar ba ta yi tsammanin ta kammala kakar a wannan matsayi ba.

A ranar 8 ga watan Nuwamban 2021 ne Howe ya karvi ragamar Newcastle United lokacin ta na matsayin ta 19 a teburin firimiyar Ingila bayan korar Steve Bruce kwanaki 16 bayan sayar da ƙungiyar ga waɗanda ake alaƙantawa da Attajiran Saudiyya kan tsabar kuɗi yuro miliyan 305.

Kafin zuwan Howe dai da kuma sauya mamallakan ƙungiyar, tawagar ta yi fama da zama a can kasan teburin firimiya musamman a watan Oktoban 2021, sai dai bayan zuba kuɗi yuro miliyan 85 wajen sayen ’yan wasa an fara ganin farfaɗowarta a kakar da ta gabata inda ta kammala firimiya a matsayin ta 11.

Cikin ’yan wasan da Newcastle ta saya har da Kieran Trippier da Chris Wood da kuma Bruno Guimaraes baya ga Dan Burn waɗanda suka taimakawa matuƙa wajen sauya zubin wasan ƙungiyar.

Cikin wannan kakar, wasanni 5 kacal Newcastle United ta yi rashin nasara a cikinsu matakin da Eddie Howe ke bayyana cewa sun shiryawa gasar ta kofin Zakarun Turai tsaf.