Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau
Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe manoma sama da 20 a yankin Gidan Goga da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar wa wakilinmu faruwar hakan ta wayar tarho.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun kai farmaki kan manoman ne bayan da suka shagaltu da aikin noma a ranar Laraba inda suka yi yunƙurin yin garkuwa da wasu daga cikinsu.
“’Yan bindigar sun far musu ne a ƙoƙarinsu na yin garkuwa da wasu manoma amma sun fahimci cewa manoman sun fara gudun neman tsira, ganin haka sai suka fara harbin su ɗaya bayan ɗaya, kuma kamar yadda nake magana da ku yanzu, muna da gawarwakin mutum 22 da aka kashe,” in ji shi.
Ya kuma kawar da fargabar sake afka wa al’umma da ‘yan bindigar ke yi, yayin da ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da na jihohi da su kawo musu ɗauki cikin gaggawa.
Ya ƙara da cewa, “Waɗannan ‘yan ta’addan da suka firgita sun yi alƙawarin sake kai munanan hare-hare a kan al’ummarmu, kuma muna kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta kawo mana agaji kafin lamarin ya kure.”
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu.
A cewarsa, mutane tara ne suka mutu, biyar sun jikkata kuma a halin yanzu ana kula da lafiyarsu.
“Kamar yadda nake magana da ku yanzu, an kashe mutane tara, kuma tuni an tura haɗaɗɗiyar tawagar jami’an tsaro zuwa yankin yayin da al’amura suka koma daidai a yankin,” in ji jami’in.