An sako ragowar ’yan matan Sakandaren Yauri

Bayan kwanaki 707, ragowar ’yan matan Sakandaren Birnin Yauri da aka yi garkuwa da su sun shaƙi iskar ’yanci.

Majiyarmu ta ce an sako ragowar ‘yan matan biyu, Faida Sani Kaoje da Safiya Idris ne bayan tattaunawa mai zurfi da kwamitin da iyayen yaran suka kafa ya yi tare da ’yan bindigar.

A baya, gawurtaccen ɗan bidiga da garkuwa da mutane, Dogo Gide, ya ƙeƙashe ƙasa inda ya ce tilas sai Gwamnatin Jihar Kebbi ta cimma buƙatunsu kafin sako ragowar ‘yan matan da ke hannunsu.

Idan za a iya tunawa Manhaja ta ruwaito labarin sako wasu huɗu daga cikin ’yan matan ne a ranar 22 ga Afrilun bana, inda suka dawo gida da goyo bayan an biya Dogo Gide fansa mai kauri.

Makonni bayan haka ne ’yan bindigar suka sake sako wasu uku daga cikin ’yan matan, wato Elizabeth Ogechi Nwafo da Esther Sunday da Aliya Abubakar.

Nan ma an ce sai da aka biya maƙudan kuɗi kafin aka sako ’yan matan.

A farkon wannan shekarar iyayen yaran da lamarin ya shafa suka fitar da wata wasiƙar neman tallafin ’yan Nijeriya kan tara kuɗi Naira miliyan wanda za su yi amfani da shi wajen kuɓutar da yaransu daga hannun ’yan bindiga.