Sabon Mataimakin Shugaban Hukuma kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Hukumar Kula da Harkokin Kimiyya da Injiniya ta Ƙasa (NASENI), Dokta Bashir Gwandu, ya koma ofishinsa a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Litinin, 22 ga Mayu, 2023.
Gwandu ya samu wannan matsayi ne biyo bayan naɗin da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi masa, inda ya karɓi ragamar gudanar da hukumar daga hannun Mrs. Nonyem Onyechi, wadda ta kasance mai kula da hukumar kafin naɗin nasa.
Naɗin Gwandu na ƙunshe ne a cikin wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 19 ga Mayu, 2023 da lamba SGF.51/S.4/T/93 wadda Ofishin Sakataren Gwamnantin Tarayya ya aika masa.
Sanarwar da ta fito ta hannun Daraktan yaɗa labarai na NASENI, Mista Olusegun Ayeoyenikan naɗin Bashir Gwandu ya biyo bayan ƙarewar wa’adin shugaban hukumar, Engr. Prof. Mohammed Sani Haruna ne a watan Afrilun da ya gabata.
Sanarwar ta ƙara da cewa sabon matsayin Dr. Bashir Gwandu a matsayin shugaban NASENI ya fara aiki ne 12 ga Mayu,2023.