24
May
Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya ƙaddamar da katafariyar gadar sama mai ɗauke da manyan hanyoyi. Masari ya ƙaddamar da gadar ce a ranar Talata a unguwar G.R.A dake babban birnin jihar, wadda aka gina kan kuɗi Naira biliyan 6.4. An fara gina gadar ne a watan Mayu na shekarar da ta gabata, aikin na ɗaya daga cikin manyan ayyukan gina hanyoyi uku da gwamnatin jihar ta gudanar a babban birnin jihar. Da yake jawabi a wajen taron, gwamna Masari ya bayyana cewar gwamnatinsa ta gina irin waɗannan manyan gadoji na ƙarƙashin ƙasa guda…
