Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya zama shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa.
An zaɓi Inuwa a wannan muƙamin ne yayin taron da mambobin ƙungiyar suka yi a ranar Talata.
Da wannan, Inuwa ya zama wanda zai ci gaba da jan ragamar ƙungiyar nan da shekaru masu zuwa.