Illolin da suke fuskantar mata masu cin amanar aure

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da haxuwa a wani sabon makon a filinmu na zamnatakewa wanda ke zuwar muku kowanne mako a jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A wannan makon za mu ɗora daga inda muka tsaya a makon da ya gabata. A makon da ya gabata mun fara tattaunawa a kan wannan maudu’i na abin ƙyama wato zinar matan aure. A gaskiyar Magana, matan aure da dama sun afka cikin wannan ƙazantaccen ibtila’i na satar hanya. A wancan makon mun kawo muku wasu dalilai da suke sa matan aure su ci amanar aure. Sannan mun yi alƙawarin kawo muku illolin da ke tattare da shi, da kuma hanyoyin da za a kauce masa. A sha karatu lafiya.

Illolin da ke tattare da zinar matan aure

Kamar yadda na faɗa a makon da ya gabata a kashi na farko na wannan maudu’in, zinar matar aure ta fi illa sosai a kan ta mijinta. Duk da dai dukkansu suna da illa ga auren da al’umma da kuma zunubi mai girma a wajen Allah. Don haka, illolinta ba za su taɓa ƙirguwa ba. Wasu daga ciki sun haɗa da:

·Babban laifi ne mai girma da Allah ya tanadar mata azaba mai tsanani a lahira, da hukunci mai girma a Duniya. Akwai faɗar Annabi Sallallahu alaihi wasallama da yake nuna cewa, zina fitar imani ne gabaɗaya. Allah ya kiyashe mu. Don haka, sai ki kyaye ke mai aure da kike sha’awar yin tarayya da wasu mazan bayan mijinki.

·Tarwatsa gida: Zinar matar aure tana tarwatsa gida. Kamar yadda na faɗa a wancan makon, mace zuciyarta don mutum guda aka yi ta. Ba zai yiwu ta so maza biyu a lokaci guda ba. Sai dai za ta iya riqe maza fiye da ɗaya a lokaci guda, in dai kowanne da amfanin da yake mata amma ba da sunan so ba. Matar aure idan ta afka so da sha’awar wani za ka ga ta yi wasarere da nata mijin, da kuma al’amuransa gabaɗaya. Daga nan sai zaman gidan ya qi mata daɗi da ita da mijinta gabɗaya. Ka ga ba zancen farin ciki ko nutsuwa. Domin mace ce uhin gida gabaɗaya. Ya kamata mata su sani, zavar yin alfasha da aure a kanki kamar ba da zaɓi ne tsakanin zaman lafiyar aurenki da kuma jin daɗi na ƙalilan ɗin lokaci. Kuma ba kanki za ki sa a ƙunci ke kaɗai ba. Har ma da iyalanki baki ɗaya za ki ƙuntata. Su ma su ji su cikin ƙunci da rashin walwala.

·Kawo wa miji yaran da ba nasa ba: Ɗaya daga cikin manyan illolin zinar matan aure shi ne, kawo wa mijinta yaran waje waɗanda ba nasa ba, kuma ya raine su a matsayin nasa na cikinsa. Wannan zalunci ne ƙarara da cin amana har a wajen Allah.

·Tsiya: Kamar yadda Annabi Sallallahu ya faɗa, da zina da arziki ba sa tava kasancewa tare, to haka abin yake. Ko mace ko namiji, mai aure ko mara aure, to ba ke ba arziki mai alkhairi. Ko kin yi arzikin ma na haram ne. Kuma da wanne ido za ki kalli Allah?

·Mutuwar aure: ‘yar uwa mai cin amanar aure ki sani, aurenki yana tangal-tangal. Da ma daga sanda kika fara neman maza a waje, ki sani, ko ba daɗe, ko ba jima, wataran asirinki zai tonu. Daga ya tonu kuma, ba namijin da zauna da mace mazinaciya. Za a sake ki cikin tozarci. Kuma duniya ta san me kika yi.

·Dawwama a bakin ciki da rashin kwanciyar hankali: ‘Yaruwa, duk yadda kike ganin kina cikin ƙunci a gidan aurenki, kuma kike tsammani tarayya da wani namjin na waje ita za ta kawo miki farin ciki da walwalar da kike nema, to ki sake tunani. Zina ba ta kawo komai sai baƙin ciki da rashin kwanciyar hankali dawwamammu. Ke dai idan za ki yi, ki yi, amma fa ba zancen wai ki ji daɗi ko huce takaicin mijinki. Gara idan ba kya jin daɗi ko samun gamsuwa a wajen mijinki, to kawai ku rabu shi ya fi.

·Tozarci da zubar da mutuci daga ke har ‘ya’ya: Macen duk da ta sake ta yi yawon banza, walau a gaban iyayenta ko a gidan miji, ki sani ba zancen mutunci daga kan ki har ‘ya’ya da jikokinki. Namiji shi sai ya yi, abin ya zame masa ado. Ke ko yanzu za ki ji ki a bakin duniya. Kuma a goranta wa yaranki da jikokinki. Wasu ma sanadiyyar haka su rasa mai aurensu. To wa gari ya waya?

·Kangara/fandarewa: Zina tana busar da zuciyar masu yin ta su kangare, su kuma fanɗare. Wasu matan na zaune da mazansu lafiya har ma da dangi da mutanen gari. Aikata mummunar ɗabi’ar yana busar da zuciya. Tun ana yi a voye, har zuciya ta bushe, a dinga yi a fili. Ibada ma ta gagara saboda bushewar zuciya. Annabi sallallahu alaihi wa sallama ya yi gaskiya, a kan cewa, aikata zina, alamar fitar imani ce.

·Cin amana: Aikata zinar matar aure kai tsaye cin amana ce. In dai kina tsoron Allah kuwa, ba za ki ci amana ba. Akwai hadisin Annabi sallalahu alaihi wa sallama da ya ce, alamomin munafukai guda uku ne: ƙarya, karya alƙawari da kuma cin amana. To ya za ki so zama cikin munafukai da Allah ya ce suna a can ƙarƙashin wuta?

·Damfara: Haka matar aure mai neman wasu mazan tana cikin haɗarin gamuwa da mazambata. Wani idan ya so ya damfare ta kuɗaɗe, zai iya ɗaukar hotunanta na tsiraici ya yi mata barazana da cewa, zai bayyana su ga mijinta ko wani. To don Allah kunyar duniya kenan. Ina ga ta lahira fa? Wata haka zai ta yawo da hankalinki har sai ta tatike ta. Wani kuma duk da hakan ma sai ya nuna. Za ta zama cikin tashin hankali da rashin yadda za ta yi. Da ma Bahaushe ya ce, da muguwar rawa, gwamma ƙin tashi.

A nan za mu dakata, sai mako mai zuwa idan rai ya kai. 08024859793