Masari ya ƙaddamar da gadar sama ta N6.4bn a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya ƙaddamar da katafariyar gadar sama mai ɗauke da manyan hanyoyi.

Masari ya ƙaddamar da gadar ce a ranar Talata a unguwar G.R.A dake babban birnin jihar, wadda aka gina kan kuɗi Naira biliyan 6.4.

An fara gina gadar ne a watan Mayu na shekarar da ta gabata, aikin na ɗaya daga cikin manyan ayyukan gina hanyoyi uku da gwamnatin jihar ta gudanar a babban birnin jihar.

Da yake jawabi a wajen taron, gwamna Masari ya bayyana cewar gwamnatinsa ta gina irin waɗannan manyan gadoji na ƙarƙashin ƙasa guda biyu, waɗanda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya buɗe cikin watan Janairu na bana a Ƙofar Ƙwaya kan kuɗi Naira biliyan 2.8 da kuma Ƙofar Ƙaura abkan kuɗi Naira biliyan 2.9.

Gwamnan ya kuma ce tun farko an bayar da aikin gina gadar dake G.R.A a kasafin kuɗi na shekarar 2022 kan kuɗi N4.3bn, sai dai daga baya an sake duba kwangilar aikin inda aka bayar da ita kan kuɗi N6.4bn saboda diyya da aka biya mutanen da aikin zai shafa da kuma ƙarin wasu aiyuka da za a gudanar a wajen.

“Duka aiyukan da aka bayar sun kammalu inda masu ababen hawa da sauran masu amfani da hanyar tuni suka fara morar aikin. Wannan roman dimokaraɗiyar ya samu ne a lokacin mulkin jam’iyyar APC, wanda alƙawari ne ta ɗauka lokacin yaƙin neman zave,” inji shi.

Masari ya kuma ce aiyukan sun inganta rayuwar al’umar jihar, a cewarsa maƙasudin gudanar da waɗannan aiyukan shi ne don sauƙaƙa zirga-zirgar ababen hawa a birnin.

Haka zalika, ya ƙaddamar da sabuwar hanya da gwamnatinsa ta gina mai tsawon mitoci 900 da ta tashi daga unguwar Ƙofar Guga zuwa Sulluɓawa ta dangane da Masanawa dake a birnin na Katsina.

Inda hanyar ta lashe kuɗi har Naira biliyan 1.3, wanda ya haɗa da diyyar da aka biya mutanen da aikin ya shafi gidaje da shagunansu.

Daga ƙarshe, Masari ya gode wa al’umar jihar bisa sake zaɓen jam’iyyar APC da suka yi a zaɓukan da suka gabata, daga nan sai ya tabbatar wa al’umar jihar cewa, magajinsa wato Dikko Umar Raɗɗa zai ɗora da irin waɗannan ayyukan alheri daga inda ya tsaya.