Ganduje ya rushe majalisarsa mako guda kafin miƙa mulki

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya bai wa ‘yan majalisarsa masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnati da su miƙa ofisoshinsu kamar yadda doka ta tanadar.

Umarnin na ƙunshe cikin sanarwar da Gwamnan ya fitar ranar Litinin ta ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar kuma mai ɗauke da sa hannun Babbar Sakatariya, Hajiya Bilkisu Maimota.

Wannan na zuwa ne yayin da ya rage ƙasa da mako guda kafin ƙarewar wa’adin mulkin Gandujen.

Ganduje ya umarci duka kwamishinoninsa, masu ba shi shawara na musamman da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa da sauransu, da su miƙa ofisoshinsu ga manyan sakatarori da daraktocin gudanarwa da ke ma’aikatunsu.

Kazalika, ya umarci waɗanda lamarin ya shafa da su miƙa baki ɗayan kayan gwamnatin da ke hannunsu kada ya wuce ranar 26 ga Mayu, 2023.

Haka nan, ya umarce su da su samar da kwafin bayanan miƙa ragamar ofisoshin nasu ga ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar.