Ban shigo Kannywood don neman kuɗi ba – Sadiya Sokoto

Daga IBRAHIM HAMISU

Sadiyya Muazu wacce aka fi sani da Sadiya Sokoto, jaruma ce da ta ke tashe a masana’antar fim ta Kannywood, musamman a fim ɗin ‘Rumfar mai Shayi’. A tattaunawarta da wakilin Manhaja a Kano, za ku ji tarihinta da kuma faɗi-tashin da ta yi har zuwa wannan lokacin. Ku biyo mu:

MANHAJA: Da wa muke tare?

SADIYA SOKOTO: Sunana Sadiya Muazu, wadda aka fi sani da Sadiya Sokoto.

Ko za ki ba mu taqaitaccen tarihinki?


Ni ‘yar asalin Sakkwato ce, amma yanzu Ina zaune a Kano, na yi Primary da Secondary dukka a Sokoto, sannan na yi diploma akan aikin Jarida a Sokoto Politechnic.

Ta yaya aka samu kai a masana’atar fim ta Kannywood?

To na shiga masana’atar fim ta Kannywood kusan shekaru huɗu da suka gabata.

Menene ya sa ki sha’awar shiga masana’atar Kannywood?

Ni gaskiya fim burge ni yake yi yadda na ke ganin ‘yan fim suke acting musamman mata abin yana burge ni, kuma gaskiya ni ban shigo fim don kuɗi ba, ni dai kawai fim ya na burge ni.

Wasu na shigawo Kannywood da niyyar neman kuɗi, wasu kuma da niyyar faɗakarwa. Ke da me ki ka shigo?

Ni da niyyar faɗakarwa da kuma sha’awa na shigo, kuma kowa zai so ace a inda yake sana’a ya zama wani abu. Amma ni tun lokacin da na shigo manyan Kannywood suna gaya min cewa kar na yi gaggawa, “idan kina da rabo za ki ci abinci,” ya zuwa yanzu gaskiya Alhamdulilahi, mun fara cin abinci.

Ya zuwa yanzu finafinai nawa ki ka yi?

Na yi finafinai da ɗan dama, duk da yake wasu sau ɗaya ko biyu na ke fitowa, amma a ƙalla za su kai takwas. Daga ciki akwai ‘A duniya’, ‘Kwana 90’, ‘Tsangayar Malam’, ‘Rumfar Mai Shayi’, ‘Wata Nahiya’. Da yawan mutune a fim ɗin ‘kwana 90’ ne suka san na fara fim, amma a nan gaba kaɗan za a san wacce ce Sadiyya Sokoto da izinin Allah.

Menene burinki a Kannywood?

Burina a fim shi ne, na faɗakar na nishaxantar, sannan na yi fice.

Waɗanne irin nasarori za ki iya cewa kin samu a Kannywood?

Nasarori kam na gode Allah, tun da a gaskiya Ina samun na rufin asiri, za mu yi aiki a bani haƙƙina, na je na tushe wata lalura, ka ga kuwa ai Alhamdulilahi, ba wai sai ka samu mai yawa ba, amma a hankali a hankali sai ka ga mutum ya kai inda bai yi tunani ba. Ka ga babu abinda zance sai godiya.

Waɗanne irin ƙalubale ki ka fuskanta daga lokacin da ki ka fara zuwa yanzu?

Ƙalubale kusan zan iya cewa, ƴan kaɗan ne, da yake daman manyanmu su na gaya man cewa mu yi haƙuri, amma ba wanda ya taɓa yi min wulaƙanci ko ya ci zarafi na a Kannywood. Saboda ni Ina da wata ɗabi’a wacce duk wanda ya yi min wani abu to bazan ɗaga wurin ba sai na gaya maka, saboda ni ba na so na kwana da kowa a raina, kuma ba na so wani ya kwana da ni a rai.

Daga cikin finafinan ki wanne ne ya fi burge ki?

Eh a gaskiya Ina alfahari da fim ɗin ‘Wata Nahiya’, domin shi ne fim ɗina na farko da na taka rawa mai yawa a ciki, kuma aka bani ƙarfi a ciki. Sai kuma fim ɗin ‘Tsangayar Malam’. Wanda a gaskiya na yi rashin kirki a cikin fim ɗin.

Wacce ce babbar ƙawarki a Kannywood?

Babbar ƙawata a Kannywood ita ce Maryam ƴar gata, wacce ƴar asalin Jihar Bauchi ce, domin gaskiya ko yau na bar Kannywood ina alfahari da ita, kuma gaskiya mutum ce, ina yi mata fatan samun nasara a rayuwarta.

Kafin ki shigo Kannywood kin nemi yardar iyayenki?

Sosai kuwa, a lokacin da na fara cewa a gidanmu zan yi fim abinda babana ya fara cewa shi ne, “to Saadiyya ki yi addu’a, na san wacce ce ke, idan yin alheri ne Allah ya ba ki ikon zuwa, idan kuma ba alheri ba ne Allah ya fi mu sanin abinda ya ke ɓoye.” Sai suka ba ni wata biyu na yi addu’a, to a taƙaice tun daga ranar da muka yi da wannan maganar to kullum sai na yi mafarkin ina yin fim har zuwa lokacin da na shigo Kano na fara fim.

Wane ne maigidanki a Kannywood?

Maigidana na farko shi ne Abdulhadi Nasidi, na biyu shi ne Hamisu mai Ƙima, na uku shi ne, Sulaiman Edita, waɗannan mutanen sun riƙe ni hannu biyu-biyu kuma kowa yasan a Kannywood mutane ne masu ƙima.

Kin taɓa yin aure ne?

A’a ban taɓa yin aure ba, Ina da niyya mai ƙarfi dai.

Kin taɓa yin aure ne?

A’a ban tava yin aure ba, Ina da niyya mai ƙarfi dai.

Mun gode.

Ni ma na gode sosai.