Aƙalla mutum huɗu aka tabbatar sun mutu, sannan wasu uku sun jikkata sakamakon fashewar da ta auku a wani shagon mai welda a yankin Ƙaramar Hukumar Isa, Jihar Sakkwato.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai cewar, “Na ɗauka ‘yan bindiga ne suka shigo a lokacin da na ji ƙarar fashewar” wadda ta auku a ranar Lahadi da rana.
Da aka nemi jin ta bakinsa, Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Sanusi Abubakar, ya tabbatar da aukuwar hakan.
Ya ce mutum huɗu ne suka mutu sakamakkn iftila’in.
A cewar Abubakar, “Fashewar ba ta da alaƙa da matsalar tsaron da ta addabi yankin.
“Fashewar ta faruwa ne ta dalilin tukunyar gas da ke wani shagon welda wanda mutum huɗu sun mutu sakamakon haka.
“Mutum ukun da suka jikkata na cikin mawuyacin hali, ana ci gaba da yi musu magani a wani asibiti da ba a bayyana ba.”
