CBN ya ci tarar Bankin Sterling miliyan 218 saboda karya dokoki tara

Daga AMINA YUSUF ALI

An ci tarar Bankin Sterling kimanin kuɗi har Naira miliyan 218 million saboda saɓa wa dokoki har guda tara na Babban Bankin Nijeriya (CBN).

Wannan bayanin ya bayyana ne a cikin jawabin kuɗi na bankin na shekarar 2021 wanda aka saki a mako biyu da suka gabata.

CBN ya ci tarar Bankin Sterling Naira miliyan 62 saboda sanya bankin a ƙarƙashin NEMSF.

Haka Babban bankin ya caji Bankin Sterling ɗin ƙarin wasu kuɗaɗe 56 da kuma Naira miliyan 52 a kan sauran dokokin da ta karya.

Hakazalika, Bankin Sterling ɗin kuma ya bayyana cewa, CBN ɗin ya kuma cin tararsa ta Naira miliyan 20 a kan mallakar filin da ta gina sababbin rassanta ba tare da amincewar CBN ɗin ba.

Haka kuma an ci tarar bankin Naira miliyan 10, saboda rufe rassansa da ya yi guda biyu a shekarar 2020 ba tare da neman sahalewar CBN ɗin ba.

Sannan an umarci bankin ya biya Naira miliyan 4 a matsayin kuɗin binciken kasadar kadara a shekarar 2020.

Haka kuma wata tarar da CBN ya ci Bankin Sterling ɗin ita ce, hawan ƙawara a kan ƙa’idojin aiki da hanyoyin hada-hadar kuɗi ta lantarki a Nijeriya a watan Yunin 2020 wanda ya haddasa gyaravmatsalolin ma fi ƙarancin amfani da ATM, wanda aka nemi su biya Naira miliyan 2, a matsayin ladabtarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *