Ƙungiyar Izala ta raba wa malamai babura don shiga karkara yin da’awa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) a Jihar Gombe ta raba wa malaman ta dabura domin gudanar da aikin da’awa a yankunan karkara.

Shugaban ƙungiyar a jihar, Injiniya Salisu Muhammad Gombe ne ya jagoranci raba baburan ga wasu daga cikin malaman domin sauƙaƙe musu aikin da’awa a yankunan jihar.

Injiniya Salisu Gombe ya ce, manufar ƙungiyar ita ne na isar da saƙon Allah ga bayinSa da suke lungu-lungu a sassan jihar ta Gombe.

Ya kuma bayyana cewa, wani bawan Allah ne ya saya ƙungiyar baburan domin raba su ga masu aikin da’awa.

Da yake tsokaci kan rabon baburan, Shugaban Majalisar Malamai na Ƙungiyar, Sheikh Abubakar Abdullahi Lamido yace yana cike da farin ciki kan wannan abun alkhairi.

Sannan ya yi addu’a da fatan alheri ga wanda ya sanya dukiyarsa wajen sayen baburan domin ciyar da addinin Allah gaba.

Baburan, an raba su ne ga rassan ƙungiyar inda aka bai wa reshen JIBWIS na Jalingo Kamo da ke Ƙaramar Hukumar Kaltungo, sai aka bai wa Malam Usman Manga Kumo da Malam Muhammad Rabiu.

Daga bisani Babban Daraktan Agaji na Jiha, Alhaji Maigari Usman Malala ya yi godiya tare da kira gare su da su kara ƙaimi ga aikin isar da saƙon Allah, sannan ya sake yin kira ga al’umma da su sanya ƙungiyar cikin addu’a saboda waɗanda suke yi mata zagon ƙasa.