Tasirin motsa jiki ga lafiya (1)

Daga AISHA ASAS

Motsa jiki wata ɗabi’a ce da har yau ba ta gama zama ‘yar gida a Ƙasar Hausa ba. Har a wannan lokacin akwai waɗanda ke kallon sa a layin ɗaya daga cikin gutsiri-tsoma da bature ke rajin karewa tare da ba shi muhimmanci, wanda a wurin su duk rashin aikin yi ne.

Da yawa ba su amince cewa, atisaye na taka muhimmiyar rawa a layifar gangar jikinsu ba. Wannan ne ya sa jaridar Manhaja ta zaqulu wannan darasin don ya zama wayar da kai ga waɗanda suka jahilce shi, ya kuma ƙara wa masu yi karsashi, sannan ya zama ilimi ga masu neman ƙarin bayyani kansa.

Atisaye ko in ce motsa jiki abu ne da ya zama magani ɗaya mai warkar da cuta goma, domin tasirin sa a jikin ɗan Adam mai tarin yawa ne. kusan kowanne vangare na lafiya, motsa jiki na taka rawa a cikin sa. Sannan zai iya zama silar kawo wasu ababe da jiki ke buƙata kamar kaifin basiri, sannan zai iya kawar da wasu da jiki ke neman maraba da su kamar ƙiba ko tumbi.

Da yardar mai dukka, za mu soma da kawo wasu daga cikin alfanun da motsa jiki ke kawo wa jikin ɗan Adam, waɗanda jikin ke buƙata.

Motsa jiki na ƙara kaifin basira:

Ɗaya daga cikin romon motsa jiki akwai taimaka wa ƙwaƙwalwa wurin daidai ta kanta, tare da wanke ta ta yadda zata fi saurin fahimta da kuma aje karatu ko wasu madangantar sa.

Bari na bada misali da yara masu zuwa makaranta, idan mun lura da kyau, za mu ga yaran da ke zuwa makaranta a ƙafa, sun fi yaran da ake kai da abin hawa saurin sakewa, tare da fahimtar karatu sosai. Kuma sukan ɗara su kawo wuta yayin darasi.

Haka ma a ɓangaren tsofaffi, idan ka sa ido, za ka sami mafi yawan tsofafin da suka cika yawo ba kasafai suke saurin manta abubuwa ba, idan ka cire masu fama da cutukan ƙwaƙwalwa masu shafe tunani, kamar cutar Alzheimer (cuta ce da ke hallaka ma’adanar tunanin ɗan Adam, sanadiyyar mutuwar ƙwayoyin halitta na ɓangaren, hakan kan iya sa ruɗani a wurin bambance jiya da yau ko wanda ya shuɗe. Sau da yawa wannan cuta kan yi sanadin manta ababe masu muhimmanci, ciki kuwa hard a ‘ya’ya da iyaye.)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *