Daga Ummaru Dan Gara a Legas
Sakataran Kuɗi na Ƙungiyar ’Yan Karas a Jihar Legas, Alhaji Ummaru Dan gara Sarina ta Ƙaramar Hukumar Garko, mazaunin Unguwar mile12 da ke Legas, ya bayyana cewa, shi da sauran al’ummar kasuwar mile12 suna ƙara gamsuwa da jagorancin shugabam a kasuwar mile12, Alhaji shehu Usman jibirin samfam tare da sauran shuwagabannin ɓangarorin kasuwar ta kewayanta gaba ɗaya.
Alhaji Ummaru Dan Gara ya yi wannan tsokaci ne a gidansa da ke Sarina jim kaɗan bayan kammala karɓar baƙuncin waɗansu ɗimbin al’ummar da suka fito daga sassa daban-daban na ƙasar nan, su ka shigo jihar Kano domin taya shi murnar samun damar gudanar da addu’ar ɗaurin auren ɗiyarsa da angonta a ranar Lahadin nan da ta gabata.
Dan Gara ya cigaba da nuna farin cikinsa dangane da wannan al’amari inda ya cigaba da jin jinawa shugaban kasuwar mile12, Alhaji shehu Usman jibirin samfam Dallatun Egbaland Abeokuta da sauran shuwagabannin ɓangarorin kasuwar bisa ga ƙoƙarin da su ke yi na haɗa kawunan al’ummar kasuwar domin su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya a wajen gudanar da harkokin kasuwancin su na yau da kullum da sauran al’amuran da suka shafi rayuwarsu baki ɗaya.
Ya cigaba da janyo hankulan al’ummar kasuwar ta mile12 da su ƙara ƙoƙari wajen baiwa shugabanni girman da Allah Ubangiji ya ba su ta fannin shugabanci, domin hakan ya zamo darasi ga matasa masu tasowa da sauran makamantansu.
Bugu da ƙari, Dan Gara ya cigaba da jinjina wa shugaban ɓangaren kulawa da cigaban kasuwancin Karas da kabeji, Alhaji Bala Yaro hunkuyi bisaga jagorancin jama’a cikin adalci.
A cewarsa, babu nuna bambancin gari ko kuma jihar, ya ce, da fatan Allah Ubangiji ya cigaba da yi masa jagorancin jama’a a cikin adalci kamar yadda ya saba yi a yau da kullum.
Hakazalika, ya cigaba da jinjinawa tsohon shugaban ɓangaren kulawa da kasuwancin Karas da kabeji a Legas, Alhaji Sa,idu Dan ƙanin Bala Sarina kuma ma’ajin kasuwar mile12 gaba ɗaya.
A halin yanzu, a cewarsa bisa ga kyawawan halayensa na kishin jama’a da son cigabansu baki ɗaya tare da yin biyayya ga shuwagabanni. Da fatan Allah Ubangiji ya cigaba da yi masa sakamako na alheri.