CBN ya yi ƙarin kuɗin ruwa zuwa kashi 18.5%

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya yi ƙarin kuɗin ruwa daga kashi 18 zuwa kashi 18.5 cikin 100.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ne ya sanar da hakan a ranar Laraba bayan kammala taron kwamitin da ke kula ɓangaren a hedikwatar CBN da ke Abuja.

Wannan shi ne karo na uku da bankin ke ƙarin kuɗin ruwan.

Da yake yi wa manema labarai ƙarin haske game da batun, Emefiele ya ce ƙalubalen tsadar da ake fuskanta a fannin makashi na daga dalilan da suka haifar da ƙarin.

Masana tattalin arziki sun ce mai yiwu ƙarin kuɗin ruwan da bankuna kan ɗora a bashin sukan bayar.