Kafin a rantsar da sabuwar gwamnati

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Kwanaki kaɗan ya rage a rantsar da sabuwar gwamnati a matakin jihohi da na tarayya, a ranar 29 ga wannan wata na Mayu. Wasu Gwamnonin jihohin da suka samu tazarce za a rantsar da su a karo na biyu, kamar irin su Borno, Adamawa da Gombe. Yayin da masu sabbin gwamnoni irin su Kano, Jigawa, Katsina, Sakkwato, Zamfara, Neja da Filato, za su ɗauki rantsuwar kama aiki a karo na farko.

Hankalin ’yan siyasa da magoya bayan su ya karkata ga bikin rantsarwa, da jar miya da wasu ke tunanin za a sha da su. Ba lallai hankalin su ya kai kan yadda sabuwar gwamnati mai zuwa za ta fara kamun ludayinta ko kuma ƙalubalen da za ta iya cin karo da su ba. Lallai ne kuma mu fara tunanin haka, domin kuwa sanin kowa ne ƙasar nan na cike da ɗimbin matsaloli da kowanne shugaba yake fargabar haɗuwa da su. Matsalolin da za su iya gurgunta masa shiri da duk wani tanadi da yake da shi na gyaran ƙasar nan.

Ina so ne na yi nazari game da abin da ya kamata gwamnatoci masu zuwa su yi la’akari da shi kafin shiga ofis. Hausawa sun yi wata karin magana da ke cewa, Yaro Bari Murna Karenka Ya Kama Zaki! Ban ce kar a yi murna da samun mulki ko shugabanci ba, wannan ni’ima ce daga Ubangiji. Kuma Allah Ya ce miki ka nuna godiya ga ni’imominsa. Alhamdulillahi!!

Amma kuma bayan murna sai a zauna a yi karatun tanatsu, a dubi tulin ayyukan da ke gaba, da hanyoyin da za a ɓullo musu. Musamman a jihohin da suke da sabbin gwamnoni, irin Kano, Kaduna da Zamfara, talakawa na nan na dakon ganin kamun ludayinku. Suna son su ga irin canjin da za ku kawo musu a ɗan ƙanƙanin lokaci.

Kafin dai a ce kun kai kwanaki ɗari a kan mulki, a ga kun kawo wasu dabaru da za su magance wasu daga cikin matsalolin da suka zama musu alaƙaƙai, wanda gwamnatin baya ta kasa cimma su.

Daga zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da sabbin Gwamnoni, sabon yanka, tsoffin yankan Gwamnoni duk babu wanda bai cika talakawa da alƙawura iri-iri ba, wanda za a iya cikawa da wanda sai bayan wasu shekaru huɗun kafin a sake tunawa an faɗe suko ma dai a ce sun bi ruwa kawai. Domin kuwa babu yadda za a iya aiwatar da su a yadda aka faɗe su, in ba da wani abin da gwamnati ta ga za ta cimma moriya ba.

Lallai duk gwamnatin da za ta zo ta kwana da sanin cewa, Hangen Dala Ba Shiga Birni Ba Ne! Gidan gwamnati na da daɗi da alfarma, sannan kuma yana da nasa matsalolin. Kada kamun ludayinku ya sa jama’a su fara tunanin Gwamma Jiya da Yau! Ku yi ƙoƙari ku nemo ƙwararrun da suka san aiki, kuma aka yarda da gaskiyar su da ingancin aikin su, su taimaka muku, ko da kuwa mutanen da suka cancanta daga wasu jam’iyyun siyasa suka fito ko, ma ba asalin ’yan jihar ku ba ne, amma a nan Allah Ya ajiye su, suke rayuwa.

Lallai yana da matuƙar muhimmanci ga dukkan ‘yan Nijeriya su yi haƙuri su haɗa kai don ganin sabuwar gwamnati mai zuwa ta samu nasarorin da za su kai ga dawo wa ƙasar nan martaba da kimarta. A rungumi juna, a kawar da bambancin da yake daɗa kawo mana rabuwar kai. Mu zauna mu tattauna yadda za a tafiyar da ƙasar nan ta yadda kowanne ɓangare zai bayar da tasa gudunmawar ga cigaban Nijeriya baki ɗaya.

Muna kira ga sabon shugaban ƙasa da sabbin gwamnoni kada su manta da alƙawuran sa suka yi wa matasa da suka sadaukar da lokacin su don taya ku yaƙin neman zaɓe, da taimaka muku ta fuskoki daban-daban.

Lokaci ne yanzu na ramawa kura aniyarta. A duba waɗanda suka yi karatu a cikin su, a sama musu ayyukan yi, masu ƙaramin karatu a koya musu sana’o’i a basu jari.

Masu wata ƙwarewa ko da ta kasuwanci ce a nemi su fitar da basirarsu a gani a taimaka musu. Masu karatu a basu tallafin karatu, don su samu sauqin gudanar da karatu, da kuma ragewa iyayensu nauyi. Hatta waɗanda aka riƙa amfani da su ana razana ’yan adawa da cin mutuncin wanda ya savawa ra’ayin da ake so, su ma a taimaka musu da abin da zai nutsar da su ya dawo musu da hankalinsu, su zama mutanen kirki, da suka san ciwon kansu.

A ƙirƙiro musu da wasu hukumomi da za su iya ba su ayyukan da ƙarfin su da basirarsu za ta yi musu amfani, masu son komawa makaranta a taimaka musu su koma. Wannan shi ne ribar dimukraɗiyya, kuma haka ne zai sa jama’a su fahimci ba su yi wa siyasa wahalar banza ba.

Ina fatan gwamnati mai zuwa za ta ba da ƙarfi wajen kammala aikin haƙo man fetur a Arewa, wanda gwamnati mai barin gado ta tabbatar da samuwarsa. Aikin samar da wutar lantarki na Mambila da aikin keto da teku zuwa Arewa, duk a kammala su. Kana ga aikin shimfiɗa titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Maraɗi, da gyaran manyan hanyoyin ƙasar nan da suka yi matuƙar lalacewa

Zai yi kyau kafin a fara ƙaddamar da sabbin ayyuka, a yi bincike kan tsofaffin ayyukan da aka riga aka bayar da kwangilolinsu, don a samu a kammala su, a fara cin moriyarsu kafin a shiga wasu sababbin ayyuka, domin su ma an bayar da su ne saboda muhimmancin su ga al’umma. Gwamnatin tarayya ta mayar da hankali kan batun ƙara ɗaukar jami’an tsaro na ‘yan sanda da na soja, domin taimakawa waɗanda suke ƙasa, saboda ƙarancin su na barazana ga tsaron ƙasa, domin kuwa matsalolin tsaro kullum ƙaruwa suke yi. Kuma babu wadatattun ma’aikatan da za su iya tunkararsu har a yi nasara.

Ba zai zama Riga Malam Masallaci ba, idan na ce gwamnati ta yi nazari kan shirin canjin sabon kuɗi da taqaita amfani da kuɗi da aka ɓullo da shi dab da Babban Zaɓen 2023, wanda ya kawo ta da muƙarrabanta cikin wannan mulki. Lallai a sake duba wannan tsari da kotu ta jinginar da shi na tsawon wani lokaci, kafin ya dawo a ɗora daga inda aka tsaya.

Lallai ne a sake masa fasali ta yadda, zai samu karɓuwa a wajen ‘yan Nijeriya, kuma ba zai ƙara jefa su cikin wani ƙangin rayuwa kamar yadda a baya kowa ya ɗanɗana kuɗarsa ba.

Na san ma’aikatan gwamnati na nan na tsumayin sabuwar gwamnati a dukkan matakai, da kunnuwa buɗe, domin jin albishir ɗin da sabon shugaban ƙasa ya ce zai yi musu na ƙarin sabon albashi, don ya dace da halin rayuwar da aka tsinci kai a ciki. Lallai ne mu kuma ‘yan Nijeriya mu haɗa hannu mu yi aiki tare don ganin mun tallafawa sabuwar gwamnati mai zuwa, don ta samu sauƙin sauke nauyin da ya hau kanta na samar da cigaban ƙasa.

Allah Ya sa a yi bukukuwar karvar mulki lafiya, cikin walwala da raha da juna. Kowa kuma ya duƙufa da addu’a don yi wa ƙasa da al’ummar ta fatan alheri da samun ƙasa dunƙulalliya mai cike da albarka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *