Labarai

Nijeriya ta ƙetare iyaka a cin bashi, cewar Ofishin Kasafin Kuɗi

Nijeriya ta ƙetare iyaka a cin bashi, cewar Ofishin Kasafin Kuɗi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Kasafin Kuɗi na Tarayya, Ben Akabueze ya koka kan shirin karɓar rancen Nijeriya, inda ya ce, al’ummar ƙasar na iya shiga matsala. Akabueze ya yi wannan jawabi ne ranar Laraba a wajen taron ƙaddamar da sabbin zaɓaɓɓun ’yan majalisar wakilai na ƙasa karo na 10, a ɗakin taro na ƙasa da ƙasa (ICC) da ke Abuja. Damuwa da fargabar nasa na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa sabon buaatar neman lamunin dala miliyan 800 ga Majalisar Dokokin ƙasar domin biyan buaatun matsugunan gidaje miliyan 10.2 akan naira 5,000 kowanne.…
Read More
Ba mu da masaniyar bai wa Emefiele izinin barin ƙasa – Fadar Shugaban Ƙasa

Ba mu da masaniyar bai wa Emefiele izinin barin ƙasa – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce ba ta da masaniyar izinin fita waje ƙaro ilimi da aka ce Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele. Babban Hadimin Shugaban Ƙasa Kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Malam Garba Shehu ne ya faɗi hakan, yayin amsa tambayar jaridar Daily Trust ta ranar Lahadi. A baya, an rawaito Shehu na cewa, “Idan ma Shugaba Buhari ya bai wa Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, izinin fita ƙaro ilimi, ba mu san da haka ba. “Haka nan, sakatariyar Shugaban Ƙasar ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban…
Read More
Gwamnan Taraba ya ware Naira biliyan biyu don saye wa kansa motoci kwanaki kafin ƙarewar wa’adinsa

Gwamnan Taraba ya ware Naira biliyan biyu don saye wa kansa motoci kwanaki kafin ƙarewar wa’adinsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku, ya amince da Naira biliyan biyu don sayen motocin alfarma ga kansa, mataimakinsa, da matansu kwanaki 18 kafin ya ƙare wa’adin mulkinsa biyu. Jaridar Premium Times da ake wallafa wa a yanae gizo ta ruwaito wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta saboda tsoron kada a yi mata zagon ƙasa ta ce, an amince da hakan ne a yayin taron majalisar zartarwa ta Jiha (SEC) da Gwamna Ishaku ya jagoranta. “Gwamna Darius Ishaku a taronmu na SEC da ya gabata ya buƙaci majalisar ta amince da takardar da ya gabatar…
Read More
’Yan bindiga sun sace sama da mutum 40 a Neja

’Yan bindiga sun sace sama da mutum 40 a Neja

Wasu ’yan bindiga da ake zargin ‘yan fashin daji ne sun sace Dagacin ƙauyen Fugge, Malam Abdullahi Zaure, cikin Ƙaramar Hukumar Rijau a Jihar Neja. Bayanai sun ce maharan sun kuma haɗa da wasu mutum 49 sun yi awon gaba da su. Rahotanni daga yankin sun ce waɗanda ‘yan bindigar suka kwashe a harin na ranar Juma’a, sun haɗa da mata da ƙananan yara da kuma maza ƙalilan. Kazalika, an ce maharan sun tattara shanu a yankin sun yi gaba da su. Jaridar Vanguard ta rawaito cewar, maharan sun kai hari ƙauyen ne da tsakar rana a kan babura inda…
Read More
’Yan bindiga sun sako mutum 28 cikin 40 da suka sace a cocin Kaduna

’Yan bindiga sun sako mutum 28 cikin 40 da suka sace a cocin Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu mutane 28 da aka yi garkuwa da su a wani coci a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna a ranar Lahadi, 7 ga watan Mayu, 2023, sun shaƙi iskar ’yanci. Waɗanda sakon ɗin sun haɗa da ƙananan yara, waɗanda aka yi garkuwa da su a wani coci a ranar Lahadin da ta gabata, aka kai su inda ba a san ko ina ne ba. Sai dai wani babban jami’in ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa an sako 11 daga cikin waɗanda aka kashe a daren Laraba. Ko da yake…
Read More
Matashin Bakanon da ya auri Baturiya ya zama sojan Amurka

Matashin Bakanon da ya auri Baturiya ya zama sojan Amurka

Matashin nan ɗan Jihar Kano wanda ya auri baturiya a lokutan baya, wato Suleiman Isah, ya zama sojan Amurka. A ranar 13 ga Disamban 2020, aka ɗaura auren Isah da Janine Reimann, a lokacin yana ɗan shekara 23 yayin da matarsa ke da shekara 46. Ma'auranta sun haɗu ne a soshiyal midiya a dandalin Instagram inda suka taɓa soyayyar wata 10 kafin su yi aure.
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Gobara ta tashi a Kasuwar Abgeni a Oyo

Da Ɗumi-ɗumi: Gobara ta tashi a Kasuwar Abgeni a Oyo

Kasuwar Agbeni da ke Ibadan, Jihar Oyo, ta kama da wuta. Manhaja ta tattaro cewar gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 04:30 na asuba a ranar Lahadi. Shugaban Hukumar Kwana-kwana na yankin, Yemi Akinyemi, ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce, “Har yanzu jami'anmu na ci gaba da aikin kashe gobarar." Ya zuwa haɗa wannan labari ba a kai ga tantance ɓarnar da gobara ta tafka a kasuwar ba.
Read More
Buhari ya bai Gwamnan CBN izinin barin ƙasa gabanin rantsar da Tinubu

Buhari ya bai Gwamnan CBN izinin barin ƙasa gabanin rantsar da Tinubu

*DSS ta nuna rashin jin daɗinta kan bai wa Emefiele izinin ficewa daga ƙasa Sahihan bayanai na nuni da cewa, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya samu izinin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a kan ya tafi ƙaro ilimi a ƙetare. A cewar Sahara Reporters, hakan zai bai wa Emefiele damar ficewa daga ƙasar kafin Buhari ya bar mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023. Wanda hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin Emefiele da aikata ba daidai ba da suka haɗa da cin hanci da rashawa da kuma ɗaure wa ta’addanci gindi. Idan za a…
Read More
Nijeriya ce ta biyu a yawan mace-macen mata masu ciki

Nijeriya ce ta biyu a yawan mace-macen mata masu ciki

Rahoton Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya (WHO) ya ce, yanzu Nijeriya ita ce ƙasa ta biyu a jerin ƙasashen da ke da yawan mace-macen mata masu juna-biyu a duniya. A cewar rahoton, Nijeriya ke da kashi 29 daga cikin adadin 290,000 na mace-macen mata masu jina-biyu da ake samu duk shekara. Kazalika, Nijeriya ce kan gaba a faɗin duniya wajen aukuwar mutuwar jarirai da ƙananan yara in ji rahoton. WHO ta lissafo wasu ƙasashen da ke fuskantar yawan mace-macen mata masu ciki, jarirai da kuma ƙananan yara da suka haɗa da Pakistan, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Habasha, Bangladesh, China, Indonesia, Afghanistan…
Read More
An kai malama kotu bisa zargin cin zarafin ɗaliba ‘yar shekara tara

An kai malama kotu bisa zargin cin zarafin ɗaliba ‘yar shekara tara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata malama, Aderonke Makonde, a ranar Laraba aka gurfanar da ita a wata kotun majistare da ke Ikeja a Jihar Legas bisa zargin laifin cin zarafin wata ɗalibar makarantar mai shekara tara. Rundunar 'yan sanda ce ta gurfanar da Makonde, mai shekaru 35 kuma malama a makarantar Westgate Land Emperial Creche Nursery and Primary School da ke Mushin, Legas bisa laifin cin zarafi. Sai dai matar ta musanta zargin da ake mata. Lauyar masu shigar da ƙara, DSP Kehinde Ajayi, ya shaida wa kotun cewa Makonde ta ci zarafin ɗalibar ne ta hanyar “shasshauɗa…
Read More