Labarai

Nijeriya ta ba da himma wajen kwaso ‘yan ƙasar da suka maƙale a Sudan – NIDCOM

Nijeriya ta ba da himma wajen kwaso ‘yan ƙasar da suka maƙale a Sudan – NIDCOM

Shugabar Hukumar Kula da 'Yan Nijeriya Mazauna Ƙetare, (NiDCOM), Hon Abike Dabiri-Erewa, ta ce Nijeriya tare da haɗin gwiwar Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), sun kammala tsare-tsare don maido da ɗaliban Nijeriya da sauransu da suka maƙale a Ƙasar Sudan. Ta ce yanayi da kuma haɗarin da ke tattare da hakan ya hana kowane jirgi tashi a halin yanzu. A cewarta, da safiyar ranar Alhamis aka ƙona jiragen saman da ke filin jirgin saman Sudan sakamakon rikicin da ƙasar ke fama da shi. Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da…
Read More
Buhari ya nemi afuwar ‘yan Nijeriya game da gwamnatinsa

Buhari ya nemi afuwar ‘yan Nijeriya game da gwamnatinsa

… Ya yi wa 'yan ƙasa godiya da damar da aka ba shi… Ya yi bikin sallarsa na ƙarshe a Villa Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya nemi afuwar dukkan waɗanda gwamnatinsa ba ta yi musu daɗi ba a halin mulkinsa. Kazalika, ya nuna godiyarsa ga 'yan Nijeriya dangane da damar da suka ba shi na mulkin ƙasa har na wa'adi biyu, wato daga 2015 zuwa 2023. Ya bayyana haka ne sa'ilin da masu ruwa da tsakin mazauna Abuja ƙarƙashin jagorancin Ministan Abuja, Muhammad Musa Bello, suka kai masa ziyarar goron sallah na Idil Fitr. Da yake jawabi,…
Read More
Ɗan Majalisar Wakilai mai jiran gado, Isma’ila Maihanchi ya riga mu gidan gaskiya

Ɗan Majalisar Wakilai mai jiran gado, Isma’ila Maihanchi ya riga mu gidan gaskiya

Zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Wakilai na shiyyar Jalingo/Yorro/Zing a Jihar Taraba, Isma’ila Maihanchi, ya riga mu gidan gaskiya. Marigayin ya rasu ne da safiyar Asabar a Abuja bayan fama da rashin lafiya. Kakakin Jam'iyyar PDP, Andeta’rang Irammae, shi ne ya sanar da rasuwar. Ya ce, “Jim kaɗa bayan kammala zaɓen marigayin ya fara rashin lafiya wanda ya ci gaba da karɓar magani a Abuja" inda Allah Ya yi masa cikawa ranar Asabar.
Read More
Osinbajo ya nemi maye gurbin shaidar zama ɗan jiha da ta haihuwa

Osinbajo ya nemi maye gurbin shaidar zama ɗan jiha da ta haihuwa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi kira da a samar da kyakkyawar fahimtar juna a tsakanin masu faɗa aji, inda ya buƙaci a aiwatar da tsarin da zai inganta haɗin kan al’umma da haɗin kai a Nijeriya. Osinbajo ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata a wajen taron ba da lacca mai taken ‘Policy Making and Good Governance Lecture Series’ wanda Cibiyar Nazarin Dabaru ta Ƙasa (NIPPS) ta shirya. Yayin da ya ke magana kan batutuwan da suka shafi ƙaura, mataimakin shugaban ƙasar ya yi kira da a maye…
Read More
Abba Gida-gida ya yi miƙa saƙon goron sallah ga Kanawa

Abba Gida-gida ya yi miƙa saƙon goron sallah ga Kanawa

Daga RABI'U SANUSI a Kano Gwamnan Jihar Kano mai jiran gado, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya miƙa daƙon taya al'ummar Jihar Kano murnar kammala azumin watan Ramadan na bana. A cikin saƙo nasa, Abba Kabir ya buƙaci al'umma a cigaba da ɗabbaƙa kayawawan darussan da aka koya yayin watan azumin da ya ƙare. Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar juma'a. Sanarwar ta ce: "Ina tabbatar wa Jama'ar Jihar Kano cewa gwamnati mai jiran gado ƙarƙashin jagorancina za ta samar da hanyoyin da za su…
Read More
Goron Sallah: Babban Hafsan Tsaro ya yi wa Musulmi barka da shan ruwa

Goron Sallah: Babban Hafsan Tsaro ya yi wa Musulmi barka da shan ruwa

Daga BASHIR ISAH Babban Hafsan Tsaro na Nijeriya, Janar Lucky Irabor CFR, ya miƙa saƙon taya murnar Ƙaramar Sallah ga ɗaukacin al'ummar musulmin Nijeriya. Janar Irabor ya yi wa Musulmi barka da kammala azumin Ramadana, ɗaya daga cikin shika-shikan addinin Musulunci. Saƙon taya murnar na ƙunshe ne cikin sanarwar da Muƙaddashin Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Tsaro, Tukur Gusau, ya sanya wa hannu, mai kuma ɗauke da kwanan wata 20 ga Afrilu, 2023. Jami'in ya yi addu'ar Allah ya karɓi dukkan ibadun da Musulmi suka gabatar a watan na Ramadan, tare da yi wa Nijeriya fatan nasara. Ya yi amfani…
Read More
Korarren kwamishinanmu na Jihar Adamawa ya yi ɓatan dabo – INEC

Korarren kwamishinanmu na Jihar Adamawa ya yi ɓatan dabo – INEC

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta ce ba ta da masaniyar inda korarren Kwamishinanta na Jihar Adamawa, Hudu Ari, ya shige tun bayan abin da ya aikata yayin zaɓen cike giɓi na zaɓen gwamnan jihar. Ari ya yi riga malam masallaci wajen sanar da sakamakon zaɓen cike giɓin da aka gudanar tun kafin kammala tattara sakamakon zaɓen. A cewar INEC, “Ba mu san inda yake ba, saboda tun bayan abin da ya faru Hukumar ta aike masa da wasiƙa ta kuma kira shi a waya. Bai amsa kira ba, kuma shi bai kira ba. “Mun buƙaci ya…
Read More
Bikin Sallah: Zaɓaɓɓen Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya taya Musulmi murnar Sallah

Bikin Sallah: Zaɓaɓɓen Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya taya Musulmi murnar Sallah

*Ya buƙaci a dage da addu'a Daga WAKILINMU Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Zamfara, Mai Girma Dauda Lawal, ya aike da saƙon taya murna ga ɗaukacin al’ummar Musulmi na Jihar Zamfara da ma ƙasa baki ɗaya bisa ganin ƙarshen watan azumin shekarar 1444 da kuma bikin sallah. A wata takardar sanarwa da ofishin zaɓaɓɓen gwamnan ya fitar wadda Sulaiman Bala Idris ya sa wa hannu, Lawal ya buƙaci al’ummar Jihar Zamfara su zage damtse wurin yin addu’o’i don wanzuwar zaman lafiya a faɗin jihar. Ya ƙara da cewa, watan Ramadana zaɓaɓɓen wata ne daga Allah (SWT) a matsayin watan yin azumi da…
Read More
Akwai fursunoni 3,298 da ke jiran a zartar musu da hukuncin kisa a Nijeriya

Akwai fursunoni 3,298 da ke jiran a zartar musu da hukuncin kisa a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Nijeriya (NCoS) ta ce akwai akalla fursunoni 3,298 da aka yanke wa hukuncin kisa kuma suke zaman jiran a zartar musu da shi a gidajen kurkukun ƙasar. Kakakin hukumar na ƙasa, Abubakar Umar, ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ranar Laraba a Abuja. Ya ce galibi a Nijeriya ba a cika zartar da hukuncin ba ga waɗanda aka yanke musu ba.Ya ce, “Akwai lokutan rashin tabbas yayin da waɗanda aka yanke wa hukuncin suke ɗaukaka kara zuwa kotuna na gaba. “Fursunonin da…
Read More
Gwamnati ta ciwo bashin Dala miliyan 800 ne don sauƙaƙa wa talakawa –Ministar Kuɗi

Gwamnati ta ciwo bashin Dala miliyan 800 ne don sauƙaƙa wa talakawa –Ministar Kuɗi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An bayyana cewa babban dalilin da ya sa Gwamnatin Tarayya ta ciwo bashin Dala Miliyan 800, shi ne don a sauƙaƙe wa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwa da su ka tsinci kan su a ciki sanadiyyar annobar Korona, sauƙaƙa matsatsin da su ka fuskanta dalilin ƙarancin kuɗaɗe a lokacin sauya launin kuɗaɗe da kuma tsadar rayuwar da za a afka dalilin cire tallafin fetur da za a yi a cikin watan Yuni. Hukumar NASSCO ce ta bayyana haka, cikin wata sanarwar da kakakin ta Joe Abuku ya fiyar a ranar Laraba. Wannan kuɗaɗe dai Ministar…
Read More