Akwai fursunoni 3,298 da ke jiran a zartar musu da hukuncin kisa a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Nijeriya (NCoS) ta ce akwai akalla fursunoni 3,298 da aka yanke wa hukuncin kisa kuma suke zaman jiran a zartar musu da shi a gidajen kurkukun ƙasar.

Kakakin hukumar na ƙasa, Abubakar Umar, ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ranar Laraba a Abuja.

Ya ce galibi a Nijeriya ba a cika zartar da hukuncin ba ga waɗanda aka yanke musu ba.
Ya ce, “Akwai lokutan rashin tabbas yayin da waɗanda aka yanke wa hukuncin suke ɗaukaka kara zuwa kotuna na gaba.

“Fursunonin da ke jiran hukuncin kisa wasu daga cikinsu kan shafe kusan shekara 15 bayan yanke musu hukuncin.

“Muna da su da yawa a gidajenmu, ya zuwa yau, muna da 3,298 da suke zaman jiran a zartar musu da hukuncin. Adadinsu ya kai kusan kaso 4.5 cikin 100 na fursunonin da suke gidajen yarin Nijeriya,” inji shi.

Ya ce da yawa daga cikin irin waɗannan fursunonin sun aikata munanan laifuka ne irin su kisan kai, fashi da makami da ta’addanci da dai sauransu.

Sai dai ya ce a baya, an sami nasarar zaratr da hukuncin kisan ga mutane da dama, kafin ƙungiyoyin da ke rajin kare haƙƙin ɗan Adam su daɗa yin yawa sosai.

“Kodayake har yanzu ana yi, amma ba kasafai ake gani ba. Rabon da a aiwatar wa da wani fursuna hukuncin kisa tun a shekarar 2016 a Jihar Edo,” inji Kakakin.