21
Apr
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Kwamishinan Zaɓen Jihar Adamawa, Hudu Yunusa Ari, har zuwa lokacin da Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Alƙali Baba Usman, zai kammala bincike a kan sa sakamakon sanar da sakamakon zaɓen Gwamnan Jihar Adamawa tun gabanin a kammala tattara sakamakon zaɓen da kuma kasancewar ba shi da hurumin aikata sanarwar, kamar yadda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana. Hakan ya na qunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willy Bassey, ya fitar a…
