A yi bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali, kiran Sarkin Kano ga al’ummar Musulmi

Daga RABI’U SANUSI Kano

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana ganin jaririn watan Shawwal a jiya alhamis 29 ga watan Ramadan shekara ta 1444 Miladiyya.

Dr. Aminu Ado ya bayyana hakan ne a wa ni zama da ya gudanar da ‘yan Majalisarsa da sauran malamai, bayan tattaunawa a kan ganin jinjirin watan Shawwal.

Ya ce sun sami umarni daga mai Alfarma Sarkin Musulmi na ganin watan Shawwal wanda Juma’a ta zama 1 ga watan Shawwal 1444 AH.

Aminu Ado Bayero ya ce an samu ganin jaririn watan Shawwal din ne a Borno, Katsina, Jigawa, da Ƙasar Saudiyya.

Basaraken ya kuma ba da umarnin al’umar musulmi da su sauke azumin Ramadan sannan su ta shi da shirin fita sallar idin Ƙaramar Sallah ranar Juma’a.

Kazalika, ya buƙaci al’umar musulmi su yi bukukuwan sallah lafiya cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

Daga nan, ya yi addu’ar Allah ya karɓi ibadun da aka gabatar a watan Ramadan.

A ƙarshe, Sarkin na Kano ya yi kira da a fitar da Zakkar Fidda-kai ga duk wanda Allah ya hore wa halin yin haka.