An cafke masu laifi 44 a Kano

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Rundunar ‘Yan Sandan ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin CP Mamman Dauda, ta afke masu laifi 44 a jihar.

Cikin sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Kakakin rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya ce jami’an rundunar jami’an rundunar yaƙi da harkokin ‘yan daba a jihar, ƙarƙashin CSP Bashir Musa Gwadabe ne suka kamo masu laifin.

A cewar sanarwar, waɗanda aka damƙen sun haɗa da ‘yan fashi da makami, ‘yan daba, sai kuma masu safarar miyagun ƙwayoyi da manyan makamai.

Kiyawa ya ce galibin waɗanda lamarin ya shafa ‘yan cikin ƙwaryar Kano ne, kuma an kama su ne da kayayyakin da suka sato ko ƙwace daga hannun jama’a.

Kakakin ya ja kunnen jama’ar jihar da a guji yin ta’ammali da miyagun kwayoyi gami da makamai a lokacin bukukuwan Sallah.

“Kuma muna shawartar dukkan wani mai aikata mummunan aiki da ya tuba ko kuma ya bar jihar kano,” inji CP Dauda.

Ga ƙarin hotuna: