Goron Sallah: Babban Hafsan Tsaro ya yi wa Musulmi barka da shan ruwa

Daga BASHIR ISAH

Babban Hafsan Tsaro na Nijeriya, Janar Lucky Irabor CFR, ya miƙa saƙon taya murnar Ƙaramar Sallah ga ɗaukacin al’ummar musulmin Nijeriya.

Janar Irabor ya yi wa Musulmi barka da kammala azumin Ramadana, ɗaya daga cikin shika-shikan addinin Musulunci.

Saƙon taya murnar na ƙunshe ne cikin sanarwar da Muƙaddashin Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Tsaro, Tukur Gusau, ya sanya wa hannu, mai kuma ɗauke da kwanan wata 20 ga Afrilu, 2023.

Jami’in ya yi addu’ar Allah ya karɓi dukkan ibadun da Musulmi suka gabatar a watan na Ramadan, tare da yi wa Nijeriya fatan nasara.

Ya yi amfani da wannan dama wajen tunatar da sojoji kan buƙatar da ke akwai na ci gaba da yi wa ƙasar nan addu’ar haɗin kai da zaman lafiya.

Kana ya yaba musu dangane da ƙwazon da suke nunawa wajen yi wa ƙasa hidima yadda ya kamata.