Buhari ya nemi afuwar ‘yan Nijeriya game da gwamnatinsa

… Ya yi wa ‘yan ƙasa godiya da damar da aka ba shi
… Ya yi bikin sallarsa na ƙarshe a Villa

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya nemi afuwar dukkan waɗanda gwamnatinsa ba ta yi musu daɗi ba a halin mulkinsa.

Kazalika, ya nuna godiyarsa ga ‘yan Nijeriya dangane da damar da suka ba shi na mulkin ƙasa har na wa’adi biyu, wato daga 2015 zuwa 2023.

Ya bayyana haka ne sa’ilin da masu ruwa da tsakin mazauna Abuja ƙarƙashin jagorancin Ministan Abuja, Muhammad Musa Bello, suka kai masa ziyarar goron sallah na Idil Fitr.

Da yake jawabi, Buhari ya lissafo muƙaman da ya riƙe a cikin shekara 40 da suka shuɗe na yi wa ƙasa hidima, kama daga lokacin da yake soja har zuwa lokacin da aka sake zaɓensa Shugaban Ƙasa a 2015.

Daga ciki, ya ce ya yi gwamna a mulkin soja, ya yi minista, ya yi Shugaban Ƙasa a mulkin soja da ma dimokuraɗiyya.

Shugaban ya taɓo batun yadda aka kwaɓe shi a mulki a 1984, da kuma gwagwarmayar da ya sha na yin takarar shugabancin ƙasa sau uku, wato a 2003 da 2007 da 2011 ba tare da ya yi nasara ba.

“Na ƙalubalanci ‘yan siyasa inda na ƙarake a Kotun Ƙoli sau uku. An yi mini dariya, amma na ce ‘Akwai Allah.’

“Allah da ikonSa sai ga shi na bai wa maraɗa kunya albarkacin fasahar katin zaɓe na din-din-din (PVC),” in ji Buhari.

Shugaban Ƙasar ya jaddada cewar, dimokuraɗiyya ce tsarin mulkin da ya fi bada damammakin yin aiki tare wajen gina ƙasa.

A nasa ɓangaren, Minista Bello ya yi wa Buhari godiya dangane da baƙuncinsu da ya karɓa yayin bikin Sallah Ƙarama na ƙarshe da zai yi a Villa, da kuma bai wa mazauna Abuja da dama zarafin shiga fadar din yi masa gaisuwar sallah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *