Siyasa

INEC ta ayyana zaɓen Gwamna a Kebbi ‘Inconclusive’

INEC ta ayyana zaɓen Gwamna a Kebbi ‘Inconclusive’

Daga BASHIR ISAH Kwamishinan Zaɓe a Jihar Kebbi, Fargesa Yusuf Saidu, ya ayyana zaɓen gwamna a jihar Kebbi wanda bai kammala ba. Ya ɗora zaɓen a wannan marhalar ne saboda abin da ya bayyana da aikata ba daidai ba da aka yi a wasu ƙananan hukumomi 18 a jihar. Baturen zaɓen ya karanto wasu sassan Dokar Zaɓe da suka ba shi damar ayyana zaɓen a matsayin wandan bai kammala ba.
Read More
Sanwo-Olu ya zama Gwamnan Legas wa’adi na biyu

Sanwo-Olu ya zama Gwamnan Legas wa’adi na biyu

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta ayyana Babajide Sanwo-Olu a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamm wanda ya gudana a jihar ran Asabar. Nasarar tasa ta tabbata ne bayan da ya samu ƙuri'u 762,134, inda ya doke babban abokin hamayyarsa na Jam'iyyar Labour, Gbadebo Rhodes-Vivour, wanda ya tsira da ƙuri'u 312,329, yayin da Abdul-Azeez Adediran ya zo na uku da ƙiri'u 62,449.
Read More
Shugaban marasa rinjaye na majalisar Kano da ‘yan dabar siyasa 160 sun faɗa komar ‘yan sanda

Shugaban marasa rinjaye na majalisar Kano da ‘yan dabar siyasa 160 sun faɗa komar ‘yan sanda

Daga RABI'U SANUSI a Kano. Shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano kuma ɗan takarar kujerar majalisar jihar ƙarƙashin jam'iyyar NNPP, Hon. Isyaku Ali Danja da wasu 'yan dabar siyasa sama da 161 sun faɗa komar 'yan sanda a jihar Kano. Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da Kwamishinan'Yan 'Yan Sandan jihar mai kula da harkokin zaɓe, CP Usaini Mohammed Gumel, yake gabatar wa manema labarai waɗanda ake zargi da hannu wajen abin da ya bayyana da cin amanar ƙasa. Gumel ya ce rundunar da sauran takwarorinta a jihar sun samu nasarar kama waɗanda ake zargi da tada zaune…
Read More
Sakamakon zaɓen gwamna daga ƙananan hukumomin Zamfara

Sakamakon zaɓen gwamna daga ƙananan hukumomin Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sakamakon zaɓen gwamna ya fara fitowa daga Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya. Sakamakon ya nuna cewa, jam'iyyar PDP ne ke kan gaba duba da ƙananan hukumomi uku da INEC ta gabatar. Ya zuwa yanzu, PDP ce ke da mafi yawan ƙuri'u daga sakamakon zaɓen da ya shigo hannun majiya. A ɓangare guda, jam'iyyar PDP ta zargi APC da ƙoƙarin yiwa jami'an zaɓe barazana a wasu ƙananan hukumomin jihar. A cewar PDP, dukkan sakamakon zaɓen da aka ɗaura a kafar yanar gizo sun nuna PDP ce ya yiwa APC cin kaca. Wannan zargi na…
Read More
APC ta lashe kujeru 23 a zaɓen Majalisar Dokokin Ekiti

APC ta lashe kujeru 23 a zaɓen Majalisar Dokokin Ekiti

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jam’iyyar APC ta lashe kujeru 23 a zaɓen Majalisar Dokokin Jihar Ekiti da aka gudanar ranar Asabar. Jam’iyyar SDP ta lashe kujeru biyu a mazabar Ekiti ta Gabas 1 da Ise/Orin, yayin da kujerar a Ido/Osi 1 ba ta cika ba. Jam’iyyar PDP dai ba ta samu nasarar lashe zaɓen ba kamar yadda sakamakon da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar a ranar Lahadi. Shugaban sashen wayar da kan jama’a masu kaɗa ƙuri’a, Temitope Akanmu ne ya fitar da sakamakon zaɓen a madadin Kwamishinan Zaɓe (REC), Farfesa Ayobami Salami. INEC ta ce,…
Read More
Zaɓen Kano: Abba ya sake tsere wa Gawuna a yawan ƙuri’u

Zaɓen Kano: Abba ya sake tsere wa Gawuna a yawan ƙuri’u

Daga WAKILINMU A ci gaba da rigegeniyar da ake yi tsakanin jam'iyyun APC da NNPP wajen lashe zaɓen Gwamnan Jihar Kano, yanzu haka NNPP ta sake tsere wa APC a yawan ƙuri'u. Bayan tattara sakamakon zaɓe na ƙananan hukumomi 30, Abba Bichi Yusuf na NNPP ya samu ƙuri'u 567,135 yayin da Nasir Gawuna na APC ke da ƙuri'u 567,352, wato bambanci ƙuri'u 217 ke tsakani a halin yanzu.
Read More
Ƙaramar Hukumar Bichi ta cilla yawan ƙuri’un Gawuna sama

Ƙaramar Hukumar Bichi ta cilla yawan ƙuri’un Gawuna sama

Daga WAKILINMU Ƙuri'ar yankin Ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano, ta taimaka wajen cilla yawan ƙuri'un ɗan takarar Gwamna na APC sama wanda hakan ya sake bai wa ɗan takarar damar shige gaban takwararansa na jam'iyyar NNPP. Da fari Abba Kabiru Yusuf ne ya kasance kan gaba a yawan ƙuri'u, kafin daga bisani lamarin ya juya kan Nasir Gawuna na APC. Bayan wani lokaci NNPP ta sake shigewa gaba har zuwa lokacin da aka bayyana sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar Bichi, a cibiyar tattara sakamakon zaɓen. Daga nan ne Nasir Gawuna na APC ya sake tsere wa Abba a yawan ƙuri'u…
Read More
Yanzu-yanzu: INEC ta ce za a yi ‘inconclusive’ a Kano

Yanzu-yanzu: INEC ta ce za a yi ‘inconclusive’ a Kano

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana zaɓen ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Takai a majalisar dokokin jihar Kano a matsayin ‘inconclusive’. Jami’in hukumar, Farfesa Usman Ibrahim na Jami’ar Bayero, Kano, ne ya bayyana hakan a ofishin INEC da ke Takai a ranar Lahadi, 19 ga Maris, 2023. “Duk da cewa ɗan takarar jam’iyyar APC, Musa Ali ya samu ƙuri’u 24,573 yayin da ɗan takarar jam’iyyar New NNPP ya samu ƙuri’u 23,569, amma har yanzu ba mu da wani zaɓi da ya wuce mu bayyana zaɓen a matsayin ‘inconclusive’. “Wannan ya faru…
Read More