INEC ta ayyana zaɓen Gwamna a Kebbi ‘Inconclusive’

Daga BASHIR ISAH

Kwamishinan Zaɓe a Jihar Kebbi, Fargesa Yusuf Saidu, ya ayyana zaɓen gwamna a jihar Kebbi wanda bai kammala ba.

Ya ɗora zaɓen a wannan marhalar ne saboda abin da ya bayyana da aikata ba daidai ba da aka yi a wasu ƙananan hukumomi 18 a jihar.

Baturen zaɓen ya karanto wasu sassan Dokar Zaɓe da suka ba shi damar ayyana zaɓen a matsayin wandan bai kammala ba.