Siyasa

APC ta yi zargin ana yunƙurin daƙile tattara sakamakon zaɓe a Adamawa

APC ta yi zargin ana yunƙurin daƙile tattara sakamakon zaɓe a Adamawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jam’iyyar APC ta zargi gwamnan jihar Adamawa, Umaru Fintiri, da yunƙurin kawo cikas ga tattara sakamakon zaɓe. Idan dai za a iya tunawa, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta ɗage tattara sakamakon zaɓen gwamna daga ƙananan hukumomin har zuwa tsakar rana. Farfesa Mohammed Mele, jami’in tattara bayanai na jihar da Yakubu Ari, kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa, ne suka sanar da hakan a ranar Litinin bayan tattara sakamako daga ƙananan hukumomi 20 cikin 21. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na ƙasa, Felix Morka,…
Read More
Fintiri ya kere Binani da ƙuri’u 35,617 a ƙananan hukumomi 20 cikin 21 a Adamawa

Fintiri ya kere Binani da ƙuri’u 35,617 a ƙananan hukumomi 20 cikin 21 a Adamawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A halin yanzu Gwamna Ahmadu Fintiri kuma ɗan takarar jam’iyyar PDP ne ke kan gaba da babbar abokiyar hamayyarsa Aishatu Dahiru Binani ta jam’iyyar APC da ƙuri’u 35,617. Wannan dai ya zo ne a sakamakon ƙananan hukumomi 20 cikin 21 na jihar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta bayyana a cibiyar tattara sakamakon zaɓen jihar da ke Yola. Ana dakon sakamakon ƙaranar hukumar Fufure. Daga cikin ƙananan hukumomi 20 da aka bayyana kawo yanzu, PDP ta samu ƙuri’u a 13, inda ta samu ƙuri’u 401,115, yayin da APC ta samu ƙuri’u a…
Read More
Chimaroke Nnamani ya bar PDP jim kaɗan bayan rasa kujerar Sanata a Enugu

Chimaroke Nnamani ya bar PDP jim kaɗan bayan rasa kujerar Sanata a Enugu

Daga WAKILINMU Tsohon gwamna a jihar Enugu, Chimaroke Nnamani, ya tsallake ya bar jamiyyarsa ta PDP, bayan ya sha kaye a hannun jamiyyar LP a takarar Sanatan Enugu ta Gabas. Zaɓaɓɓen Sanatan Enugun ta Gabas, Kevin Chukwu na jam'iyyar LP ya buga Nnamani ɗan takarar jamiyyar PDP da ƙasa da ƙuri'u 69,136, yayin da Nnamani, samu ƙuri'u 48,701. An gudanar da zaɓen ne a Asabar ɗin da ta gabata biyo bayan kisan gillar da aka yi wa tsohon ɗan takarar sanatan na LP, Oyibo Chukwu, kwanaki uku kacal kafin ranar zaɓen ta ainahi wato 25 ga Fabrairu, 2023. Nnamani, a…
Read More
PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen gwamna a Katsina

PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen gwamna a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Babbar jam'iyyar hamayya a jihar Katsina, wato PDP, ta yi watsi da sakamakon zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar. Babban Daraktan yaƙin neman zaɓen Lado/Atiku, Mustapha Muhammad Inuwa ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da Jam'iyyar ta kira a birnin Katsina. Inuwa ya ce sun yi Allah wadai da sakamakon da hukumar zaɓe ta fitar a jihar. Kazalika, ya ce ba su yarda da shi ba, kuma za su garzaya kotu. "Mun ƙi karɓar wannan zaɓen, ba mu yarda da shi ba kuma ba mu amince da shi ba a…
Read More
Mohammed Bala ya zama Gwamnan Bauchi a karo na biyu

Mohammed Bala ya zama Gwamnan Bauchi a karo na biyu

Daga BASHIR ISAH Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi, ya ci zaɓen sake zama gwamnan jihar karo na biyu ƙarƙashin jam'iyyar PDP. Sakamakon zaɓen da Baturen zaɓen gwamna a jihar, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed, ya bayyana a ranar Litinin, ya nuna Gwamna Bala ya lashe ƙananan hukumomi 15 daga cikin guda 20 da jihar ke da su. Bala ya ci zaɓen ne da ƙuri'u 525,280, inda ya doke abokin hamayyarsa na APC, Air Marshal Sadique Baba Abubakar (mai murabus) wanda ya samu ƙuri'u 432,272.
Read More
PDP ta zargi Matawalle da tilasta wa jami’an INEC ƙara ƙuri’un jabu

PDP ta zargi Matawalle da tilasta wa jami’an INEC ƙara ƙuri’un jabu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jam’iyyar PDP reshen jihar Zamfara na zargin Gwamna Bello Matawalle na shirin yin maguɗin zaɓe na sahihancin sakamakon zaɓen mahaifarsa Ƙaramar Hukumar Maradun. Jam’iyyar PDP a wata sanarwa da ofishin yaɗa labarai na Dauda Lawal ta fitar, ta ce, gwamnan ya tuntuɓi manyan jami’an INEC a ƙoƙarinsa na ganin an bayyana sakamakon zaɓen. Ta kuma yi zargin cewa gwamnan, ɗan jam’iyyar APC, ba ya son amincewa da shan kaye cikin kwanciyar hankali.
Read More
Nasarata ta al’ummar Yobe ce – Buni

Nasarata ta al’ummar Yobe ce – Buni

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana nasarar da ya samu ta sake lashe zaɓen gwamnan jihar a matsayin babbar nasara ga daukocin al'ummar jihar amma ba tashi shi kaɗai ba. Gwamna Buni ya yi wannan furucin ne jim kaɗan bayan da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ayyana shi a matsayin wanda ya ci zaɓen Gwamnan jihar a ƙarƙashin jam'iyyar APC. Ya ce, “Wannan nasara ce ta ɗaukwacin al'ummar jihar Yobe, ba ni kaɗai ba." A hannu guda, Gwamna Buni ya yi kira na musamman ga 'yan hamayya da suka fafata a zaɓen…
Read More
Shugaban PDP da aka yi wa dukan kawo wuƙa a Ebonyi ya mutu

Shugaban PDP da aka yi wa dukan kawo wuƙa a Ebonyi ya mutu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban jam'iyyar PDP a Ƙaramar Hukumar Ezza ta arewa Peter Nweke, ya mutu. Nweke ya mutu ne sakamakon raunukan da ya ji bayan wasu da ake zaton ’yan dabar siyasa ne sun farmake shi a ranar Asabar, 18 ga watan Maris yayin zaɓen gwamnoni da na ’yan majalisar jihohi. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Ebonyi, Onome Onovwakpoyeya, ta tabbatar da mutuwar Nweke a ranar Lahadi, 19 ga watan Maris. Ta ce, an yi wa Nweke dukan tsiya sannan aka kwashe shi zuwa asibiti a cikin mawuyacin hali inda daga bisani likita ya sanar da mutuwarsa. Onome…
Read More
Zaɓen Nasarawa: A.A Sule ya zarce

Zaɓen Nasarawa: A.A Sule ya zarce

Daga BASHIR ISAH Ya tabbata Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa zai mulki jihar a wa'adi na biyu. A wannan Litinin Hukumar Zaɓe, INEC, ta ayyana Gwamna Sule a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar wanda ya gudana ranar Asabar. Baturen zaɓen, Farfesa Tanko Ishaya, shi ne ya ayyana Abdullahi Sule na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri'u 347,209. Inda ya doke ɗan takarar PDP, David Ombugadu, wanda ya samu ƙuri'u 283,016. Sai dai jam'iyyar PDP a jihar ta nuna rashin gamsuwarta da sakamakon zaɓen, tana mai cewa za ta ƙalubalanci nasarar da A.A Sule…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kano ta zama ta Abba Yusuf

Da Ɗumi-ɗumi: Kano ta zama ta Abba Yusuf

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe INEC, ta tabbatar da ɗan takarar gwamna na Jam'iyyar NNPP a Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar. Abba ya taki wannan matsayi ne bayan da ya samu ƙuri'u 1,019,602 wanda hakan ya ba shi damar doke babban abokin hamayyarsa na APC kuma Mataimakin Gwamnan jihar mai ci, Nasiru Yusuf Gawuna, wanda ya tsira da ƙuri'u 890,705 a zaɓen. INEC ta ce Muhammad Sani Abacha na Jam'iyyar PDP, shi ne ya zo na uku da ƙuri'u 15,957. Da safiyar wannan Litinin INEC ta ayyana Abba sabon zaɓaɓɓen Gwamnan Kano…
Read More