Nasarata ta al’ummar Yobe ce – Buni

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana nasarar da ya samu ta sake lashe zaɓen gwamnan jihar a matsayin babbar nasara ga daukocin al’ummar jihar amma ba tashi shi kaɗai ba.

Gwamna Buni ya yi wannan furucin ne jim kaɗan bayan da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ayyana shi a matsayin wanda ya ci zaɓen Gwamnan jihar a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Ya ce, “Wannan nasara ce ta ɗaukwacin al’ummar jihar Yobe, ba ni kaɗai ba.”

A hannu guda, Gwamna Buni ya yi kira na musamman ga ‘yan hamayya da suka fafata a zaɓen da su zo a haɗu a yi aiki tare domin gina jihar ta bunƙasa.

“Saboda haka ina kira ga kowa da kowa ya zo mu haɗa hannu wuri guda domin ciyar da jiharmu ta Yobe gaba,’ in ji shi.

Har wa yau, ya jaddada cewar nasara za ta ƙara masa ƙwarin gwiwa kuma ta kara tabbatar da cewa gwamnatinsa ta taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da muhimman ayyukan cigaban jihar.

“Wannan zaɓe karo na biyu shaida ce dangane da amincewar al’ummar jihar Yobe da suka nuna min, kuma zai ƙara mini karsashi wajen ƙara kwazo da himma wajen ci gaba da ƙarin ayyukan ci gaba.”

A ƙarshe, Buni ya yaba tare da miƙa saƙon godiya ga al’ummar jihar Yobe bisa amincewar da suka nuna masa wajen fitowa ƙwansu da ƙwarƙwata su sake zaɓarsa karo na biyu.