Mohammed Bala ya zama Gwamnan Bauchi a karo na biyu

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi, ya ci zaɓen sake zama gwamnan jihar karo na biyu ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Sakamakon zaɓen da Baturen zaɓen gwamna a jihar, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed, ya bayyana a ranar Litinin, ya nuna Gwamna Bala ya lashe ƙananan hukumomi 15 daga cikin guda 20 da jihar ke da su.

Bala ya ci zaɓen ne da ƙuri’u 525,280, inda ya doke abokin hamayyarsa na APC, Air Marshal Sadique Baba Abubakar (mai murabus) wanda ya samu ƙuri’u 432,272.