‘Yan daba sun ƙona gidan shahararren wawaƙi Rarara

Daga SANI AHMAD GIWA

Bayan sa’a guda da ayyana zaɓen gwamnan jihar Kano, wasu ‘yan baranda da ba a san ko su waye ba sun ƙona gidan fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara.

Rarara dai ya kasance a tsakiyar matakin yaƙin neman zaɓen Jam’iyyar APC, inda ya riƙa rera waƙa a tarurruka daban-daban yayin yaƙin neman zaɓe.

Tun farko Rarara ya kasance a sansanin ɗan takarar gwamnan Kano na ADP, Sha’aban Ibrahim Sharada, kafin ya shiga tafiyar Gawuna makonni kaɗan kafin zaɓen gwamna.

A cewar wani ganau wanda kuma mazaunin unguwar, Yusuf Abdullahi, ‘yan barandan ne suka shiga gidan inda suka fara lalata wasu kayayyaki masu daraja kafin su banka wa gidan wuta.

Sai dai bayan ‘yan mintoci, an ce ‘yan sanda sun tarwatsa ‘yan barandan amma har yanzu wutar na ci a yayin da jami’an kashe gobara suka isa wurin.

“Abin da kawai kuke ji shine ƙarar fashewar abubuwa daga gidan yayin da gobarar ke ci gaba da lalata kayayyaki,” in ji Abdullahi.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a safiyar yau Litinin ta bayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP) a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna.

Duk ƙoƙarin isa ga Rarara ya ci tura saboda bai ɗauki kiran waya da saƙon kar-ta-kwana ba.