Wasanni

Na yi nadamar rashin sayen Arsenal – Ɗangote

Na yi nadamar rashin sayen Arsenal – Ɗangote

Attajirin nahiyar Afirka kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya ce yanzu lokaci ya wuce da zai sayi ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal da ke Ingila, inda ya ce zai cigaba da zama mai goyon bayan ƙungiyar a duk lokacin da take wasa. Ɗangote ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Bloomberg, inda ya ce yana kallon wasannin ƙungiyar sosai. "A zantawarmu ta baya na ce da zarar na kammala aikin gina matatar man fetur ɗina zan koma batun sayan Arsenal. Amma yanzu lokacin wannan maganar ya wuce domin komai yanzu ya yi tsada, sannan yanzu ƙungiyar tana…
Read More
Mbappe zai yi jinya bayan raunin da ya samu – Real Madrid

Mbappe zai yi jinya bayan raunin da ya samu – Real Madrid

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta sanar da cewa, ɗan wasan Real Madrid Kylian Mbappe zai iya yin jinya mai tsawo bayan raunin da ya samu. Ɗan ƙasar Faransa, wanda ya koma Real kan fara kakar bana daga Paris St Germain ya ci ƙwallo a La Liga da suka doke Deportiɓo Alaɓes 3-2 ranar Talata. An sauya Mbappe daga karawar sauran minti 10 a tashi daga babbar gasar tamaula ta Sifaniya. Bayan da aka tashi daga wasan ne, Carlo Ancelotti ya sanar cewar yana cikin ƙoshin lafiya, Mbappe ne ya buƙaci a canje shi, saboda kada a samu matsala.…
Read More
Dalilina na saka Rashford a benci a wasan Palace – Ten Hag

Dalilina na saka Rashford a benci a wasan Palace – Ten Hag

Kocin Manchester United, Erik ten Hag ya ce ya kamata a karɓi uzurinsa kan dalilin da ya sa Marcus Rashford ya zauna a benca a wasa da Crystal Palace. Kungiyoyin biyu sun tashi 0-0 a wasan mako na biyar a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar Asabar. Tun kafin karawar Ten Hag ya sanar da cewar Rashford ya fara komawa kan ganiya, wanda ya zura ƙwallo uku a raga a wasa biyu. To sai dai kawai aka ga Rashford a benci, inda Ten Hag ya zaɓi fara amfani da Alejandro Garnacho da Amad Diallo, daga baya ne Rashford ya canji…
Read More
Haaland ya ci ƙwallo na 100 a Man City

Haaland ya ci ƙwallo na 100 a Man City

Erling Haaland ya zura ƙwallo na 100 a raga a Manchester City ranar Lahadi a wasan da suka yi 2-2 da Arsenal a Firimiyar Ingila. Shi ne ya fara cin Arsenal a karawar ta hamayya a Etihad, kuma na 10 a kakar nan, sh ne kan gaba a yawan zura ƙwallaye a bana da fara babbar gasar tamaula ta Ingila. Dan wasan tawagar Norway ya ci na 100 a City a karawa ta 105 a kaka biyu tun bayan da ya koma Etihad daga Borussia Dortmund. Haaland na taka rawar gani a bana a Premier League da 10 a raga…
Read More
Barcelona ta lashe wasannin La Liga sau shida a jere

Barcelona ta lashe wasannin La Liga sau shida a jere

Barcelona ta je ta doke Villareal 5-1 a wasan mako na shida a La Liga ta ci gaba da jan ragamar teburi da lashe dukkan wasa shida da fara kakar nan. Kenan Barcelona ta ci gaba da buga babbar gasar tamaula ta Sifaniya da ƙafar dama a bana, koda yake mai tsaron ragarta, Marc-Andre ter Stegen ya ji raunii. Robert Lewandowski ne ya fara zura biyu a raga, sannan ya ɓarar da fenariti, haka shima Raphinha biyu ya zura a raga a wasan da wadda Pablo Torre ya ci. Ter Stegen, mai shekara 32 ya ji rauni tun kan hutu,…
Read More
Tsohon ɗan bayan Manchester United Varane ya yi ritaya

Tsohon ɗan bayan Manchester United Varane ya yi ritaya

Tsohon ɗan wasan bayan Manchester United, Real Madrid da Faransa, Raphael Varane, ya yi ritaya daga buga ƙwallo yana da shekara 31. Varane ya koma Ƙungiyar Como ta Italiya kyauta a watan Yuli amma ya ji rauni a gwiwarsa a wasansa na farko da Sampdoria a watan jiya. Ɗan wasan bayan ya ce zai ci gaba da zama a ƙungiyar amma ba zai taka leda ba. Varane ya fara taka leda a Lens ta Faransa amma ya shafe kakar wasa ɗaya a ƙungiyar ta farko kafin ya koma Real Madrid a shekarar 2011. Ya ji daɗin zama na tsawon shekaru…
Read More
Ba zan yi ritaya ba saboda na sha kashi – Anthony Joshua

Ba zan yi ritaya ba saboda na sha kashi – Anthony Joshua

Daga USMAN KAROFI Anthony Joshua ya bayyana cewa ba shi da niyyar yin ritaya daga wasan dambe bayan da ya sha kaye a hannun Daniel Dubois ranar Asabar. Dubois ya yi waje da Joshua a zagaye biyar a Wembley a daren Asabar. Wannan shi ne karo na huɗu da Joshua ya sha kashi a fagen wasan. Da aka tambaye shi ko zai sake fafatawa a shekara mai zuwa, Joshua ya ce a taron manema labarai "Wataƙila kuna tambaya ko har yanzu ina son ci gaba da wasan dambe, ba shakka ina son ci gaba da dambe. Ya bayyana cewa shi…
Read More
Kane ya zura ƙwallo a kowacce ƙungiyar Bundesliga

Kane ya zura ƙwallo a kowacce ƙungiyar Bundesliga

Harry Kane ya kafa tarihin cin ƙwallaye da yawa a Bundesliga cikin sauri, bayan da Bayern Munich ta je ta lallasa Holstein Kiel 6-1 ranar Asabar. Tsohon ɗan wasan Tottenham ya zura uku rigis a wasan, ya haura Erling Haaland mai tarihin da tazarar karawa takwas, kafin ya zura 50 a raga a Bundesliga. ƙwallo ukun da ya zura a ragar Holstein Kiel ranar Asabar, kenan ya ci 50 a wasa 35 jimilla, sai a karawa ta 43 Haaland ya zura 50 a raga a Bundesliga. Kane ya koma buga Bundesliga kan fara kakar bara daga Tottenham a matakin mai…
Read More
Mbappe ya ƙi amincewa da tayin sulhu kan taƙaddamar da ke tsakaninsa da PSG

Mbappe ya ƙi amincewa da tayin sulhu kan taƙaddamar da ke tsakaninsa da PSG

Lauyoyin ɗan wasan Faransa Kylian Mbappe, sun ce sun ƙi amincewa da buƙatar Hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar LFP, na shiga tsakanin ɗan wasan da tsohuwar ƙungiyarsa ta PSG, kan taƙaddamar rashin biyansa wasu haƙƙoƙinsa. Mbappe dai ya yi ikirarin yana bin ƙungiyar kuɗin da suka kai Euro miliyan 55, sai dai ƙungiyar ta PSG ta ce ɗan wasan ya yafe mata waɗannan kuɗaɗe a watan Agustan shekarar bara. A ranar Laraba ne dai lauyoyin ɓangarorin biyu suka gana, bayan da Mbappe ya gabatar da ƙararsa a gaban kwamitin kula al’amuran shari’a na hukumar ta LFP, lamarin da ya sa taso…
Read More
Ten Hag ya caccaki Ronaldo game da sukar Manchester United

Ten Hag ya caccaki Ronaldo game da sukar Manchester United

Kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United, Erik ten Hag ya yi watsi da kalaman tsohon tauraron ƙungiyar Cristiano Ronaldo inda ya ce shi fa ko kaɗan surutai daga waɗanda ba wasu a cikin United ba basa ɗaɗa shi da ƙasa. Tun farko Ronaldo ya yi kakkausar suka ga Manajan bayan kalamansa da ke cewa ƙungiyar ba ta saran lashe ko wanne kofi a bana, inda ya ce sam irin kalaman bai kamata ya fito daga bakin Hag ba. Duk da cewa shi kansa Ronaldon yayin wata hira da tsohon abokin wasanshi Rio Ferdinand ya bayyana cewa ba ya tunanin…
Read More