20
Feb
Daga CRI HAUSA An yi bikin rufe gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu karo na 24 a Beijing a daren yau Lahadi, inda shugaban ƙasar Sin Xi Jinping da shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na ƙasa da ƙasa Thomas Bach suka halarci bikin. A jawabin da shugaban kwamitin wasannin Olympic ta ƙasa da ƙasa IOC, Thomas Bach, ya gabatar a bikin rufe gasar, Bach ya bayyana gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing da cewa “ta musamman ne." A gun bikin rufe gasar, an kuma damqa tutar Olympic ga magajin garin Milan da na Cortina d'Ampezzo, biranen da…