26
Jun
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rahotanni daga Birtaniya da Amurka sun nuna cewa, Gareth Bale ya koma Los Angeles FC bayan ya bar Real Madrid. Jaridar Los Angeles Times, ta nakalto majiyar Major League Soccer tare da sanin yarjejeniyar ta ce, tauraron mai shekaru 32 zai iya buga wasa a LAFC daga ranar 1 ga watan Yuli. A halin da ake ciki, ESPN ta ruwaito cewa, Bale zai tashi zuwa Los Angeles a ƙarshen mako mai zuwa don sanya hannu kan yarjejeniyar da za ta ƙare a ƙarshen kakar wasa ta bana, tare da zaɓin ƙarin shekara. Bale ya taɓa zama…