Wasanni

Pele ya yi bankwana da iyalansa akan gadon asibiti

Pele ya yi bankwana da iyalansa akan gadon asibiti

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An ga fitaccen ɗan wasan ƙasar Brazil, Pele, yana bankwana da iyalansa da abokan arziki daga gadon asibiti a cikin wani faifen bidiyo. Yanayin jikin zakaran wasan ƙwallon ƙafar duniya, wanda da ya ɗauki kofin zama zakara sau uku ya tayar da hankali. Bidiyon ya nuna shi yana faman numfashi da ƙyar. Ɗan shekaru 82, wanda aka cire masa wata cuta daga hanjinsa a watan Satumbar 2021, an kwantar da shi a Asibitin Isra'ila Albert Einstein a Sao Paulo a ranar 29 ga Nuwamba, 2022. Ya kasance a asibiti har ranar Kirsimeti tare da masoyansa a…
Read More
Pele zai shafe lokacin Kiristimati a asibiti

Pele zai shafe lokacin Kiristimati a asibiti

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shahararren da ƙwallon ƙafar duniya, Pele zai shafe lokacin bukukuwan Kiristimati a asibiti, kamar yadda iyali da likitocinsa suka bayyana, sakamakon magani da ake masa na cutar daji da ke ƙara ƙamari, da kuma matsalar ƙoda da zuciya. Sanarwa daga asibin Albert Einstein na birnin Sao Paolo ta tabbatar da cewa Pele mai shekaru 82 na fama da matsalar zuciya da ƙoda, a yayin da ake mai maganin sankara, inda ta ƙara da cewa ba ya ɓangaren rai kwakwai, mutu kwakwai na asibitin. Pele wanda ake wa kallo a matsayin ɗan ƙwallon ƙafar da ba a…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Argentina ta lashe Kofin Duniya

Da Ɗumi-ɗumi: Argentina ta lashe Kofin Duniya

A ranar Lahadi aka buga wasan ƙarshe na gasar cin Kofin Duniya da aka gudanar a ƙasar Qatar. An buga wasan ƙarshen ne tsakanin Argentina da Faransa. Bayan fafatawa na tsawon minti sama da 100 a wasan, a ƙarshe Argentina ta yi nasara a kan Faransa, inda ta doke ta a bugun daga kai sai mai tsaron gida. Yanzu dai ya tabbata Argentina ce ta zama gwarzuwa a gasar wannan karon. Cikakken bayani na nan tafe...
Read More
Wani ɗan Kenya ya mutu bayan faɗowa daga saman filin wasan Qatar

Wani ɗan Kenya ya mutu bayan faɗowa daga saman filin wasan Qatar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wani ɗan ƙasar Kenya, ya mutu bayan da ya faɗo daga saman ginin filin wasan na Lusail da ke ƙasar Qatar. Qatar da ke karɓan bakwancin Gasar neman kofin duniya ta sanar da soma bincike kan mutuwar John Njau Kibue mai shekara 24. Bayanai sun ce matashin ya ji rauni sosai sakamakon faɗowar da ya yi daga saman ginin a ranar Asabar, jim kaɗan bayan da ƙasar Argentina ta lallasa Croatia a wasan kusa da ƙarshe na Kofin Duniya. Rahotanni daga yankin sun ce, jami’an ba da agajin gaggawa ne suka fara duba John bayan faruwar…
Read More
Ronaldo ya yi fatan Morocco ta ɗauki Kofin Duniya na 2022

Ronaldo ya yi fatan Morocco ta ɗauki Kofin Duniya na 2022

Dag BASHIR ISAH Fitaccen ɗan ƙwallon ƙafar nan na ƙasar Brazil, Ronaldo Nazario de Lima, ya yi fatan ƙasar Morocco ta lashe Gasar Kofin Duniya da ke gudana a Qatar. Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Morocco, Atlas Lions ce ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta taɓa kaiwa matakin na kusa da ƙarshe a tarihin gasar. Morocco ta taki wannan nasarar ce bayan da ta lallasa Portugal da ci ɗaya da nema (1-0) a fafatawar da suka yi a Filin Wasannin Motsa Jiki na Al Thumama da ke Doha. Duk da an yi waje da ƙasarsa Brazil a gasarsa, Ronaldo…
Read More
Maƙudan kuɗaɗe duk tawagar da ke Gasar Kofin Duniya a Qatar za ta samu – Rahoto

Maƙudan kuɗaɗe duk tawagar da ke Gasar Kofin Duniya a Qatar za ta samu – Rahoto

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wani rahoton Sky Sports ya bayyna cewa, Hukumar Kula da Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) ta qara yawan kuɗin kyautar da ake bai wa ƙasashen da suka samu gurbin buga gasar kofin duniya da ke gudana a ƙasar Ƙatar, da dala miliyan 40 maimakon dala miliyan ɗari 400 da ake kashewa. Tun a watan Afrilun wannan shekarar ne dai hukumar ta FIFA ta sanar da bai wa ƙasashen da suka samu gurbin buga gasar dala miliyan daya da rabi don shirya wa gasar. Haka nan kowace tawagar ƙasar da ta halarci gasar ta bana cikin 32…
Read More
Courtois ya kafa tarihi a Qatar bayan nasarar Belgium kan Kanada

Courtois ya kafa tarihi a Qatar bayan nasarar Belgium kan Kanada

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mai tsaron ragar Real Madrid da Ƙasar Belgium, Thibaut Courtois, ya kafa tarihi a Gasar Kofin Duniya na 2022 da ake gudanarwa a Ƙasar Qatar. Tawagar ƙwallon ƙafar Ƙasar Belgium ta yi aiki tuƙuru wajen kare martabarta, inda ta lallasa ƙungiyar wasan ƙwallon ƙafa ta Ƙasar Kanada da ci ɗaya mai ban haushi, ta kuma riƙe wasan a haka har aka tashi a wasan gasar kofin duniya da suka fafata a ranar Laraba. Kanada ce ta mamaye akasarin wasan na rukunin F, sai dai ta yi ta ɓarar da damarmakin saka ƙwallaye a raga, musamman a…
Read More
Ronaldo ya raba gari da Manchester United

Ronaldo ya raba gari da Manchester United

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shahararren ɗan wasan gaban Portugal, Christiano Ronaldo ya bayyana cewa, bayan cimma yarjejeniya da ƙungiyar Manchester United, ya raba gari da ita ba tare da ɓata lokaci ba. Ronaldo ya ce, "ina son Manchester United, kuma soyayyar da nake yiwa magoya baya ba za ta sauya ba." Ɗan wasan na Portugal ya ce, barin ƙungiyar ya zo masa a daidai, don haka zai cigaba da mayar da hankali a fagen ƙwallon ƙafa. Sanarwar da Ronaldo ya fitar a shafinsa na Instagram, ya ce, yana yiwa tsohuwar ƙungiyar tasa fatan samun nasarori a nan gaba. Wannan matakin…
Read More
Saudiyya ta ayyana gobe Laraba a matsayin hutun aiki sakamakon doke ƙasar Argentina

Saudiyya ta ayyana gobe Laraba a matsayin hutun aiki sakamakon doke ƙasar Argentina

Daga IBRAHIM HAMISU Sarki ƙasar Saudiyya Salman bin Abdul Aziz, ya ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu a faɗin ƙasar wani mataki na murnar samun nasara da tawagar 'yan wasan ƙwallon ƙafar ƙasar suka samu a kan ƙasar Argentina. An dai tashi wasan ne Saudiyya ta samu nasara a kan Argentina da ci 2-1 a wasan farko da suka buga a filin wasa na Lusail. Ƙasar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanar wa da ta fitar a ranarTalata. Sanarwar ta ce, Sarkin ya bayar da hutun ne domin 'yan ƙasar tun daga ma’aikatan gwamnati da ma’aikatu masu…
Read More